✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matan Saudiyya sun bijiro da bukatar dage musu dokar hana tukin mota

Mata uku da ke cikin Majalisar Shoura ta kasar Saudiyya sun bijiro da ukatar a dage wa mata dokar hana tuki a fadin masarautar.Latifa Al-Shaalan,…

Mata uku da ke cikin Majalisar Shoura ta kasar Saudiyya sun bijiro da ukatar a dage wa mata dokar hana tuki a fadin masarautar.
Latifa Al-Shaalan, daya daga cikin ’yan majalisar Shura ta Saudiyya, ta bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, cewa, ita da sauran mata biyu, wadanda suka hada da Haya Al-Mani da Muna Al-Mashir, sun bijiro da bukatar ganin majalisar ta “amince da ’yancin mata na tuka mota bisa tanadin shari’ar Musulunci da ka’idojin hanya.”
Sun kafa hujjojin bincike da suka halatta wa mata yin tuki. “babu wata doka da ta hana mata tuki. Wannan kawai riko ne ga al’ada,” a cewar Shaalan, kamar yadda ta bayyana wa AFP.