✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kashe wani mutum bisa zargin yana garkuwa da mutane

A Ranar Litinin din nan ce wasu matasa suka far wa wasu mutum hudu har suka halaka daya daga cikinsu bisa zargin cewa masu garkuwa da…

A Ranar Litinin din nan ce wasu matasa suka far wa wasu mutum hudu har suka halaka daya daga cikinsu bisa zargin cewa masu garkuwa da mutane ne a Jihar Kaduna.

Lamarin mai ban tausayi tare da tayar da hankali ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safe a kusa da gadar Kawo da ke kwaryar jihar.

Matasan sun kuma kona motar da mutanen ke ciki a yayin da su kuma ’yan sanda suka harbe wani mutum daya a lokacin da suke kokarin ceto rayuwar sauran   mutanen da ake zargin daga hannun matasan.

Sannan jami’an ’yan sandan da suka iso wajen a lokacin da ake hatsaniyar sai suka yi a kokarinsu na kora mutanen, inda hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani mutum da ke kokarin kasa kayan tiredansa a baro.

Wasu mutum uku kuma sun samu raunuka inda aka garzaya da su asibiti.

Sai dai bayan matasan sun yi aika-aikan ne aka samu labari cewa ai mutumin da suka kashe ba mai garkuwa da mutane ba ne, hasali ma sharri ne shi wanda aka ce sun biyo wai da nufin dauke shi mai suna Alhaji Musa Imam ya yi masu.

A cewar jami’an tsaro, Alhaji Musa Imam mai laifi ne da ’yan sandan Jihar Legas ke nema kuma wadanda ya yi wa sharri da sunan wai masu garkuwa da mutane ne, abokansa ne da suka tsaya masa a matsayin shaida har aka ba da belinsa a Legas bayan ya aikata laifi.

Aminiya ba ta da cikakken bayanin laifin da shi Alhaji Musa Imam ya aikata a Legas din har ta sa aka biyo shi nan Kaduna domin a tafi da shi. Sai dai bayanai sun nuna cewa su mutanen da suka tsaya masa aka bayar da belinsa din ne suka biyo shi Kaduna saboda ya daina zuwa Legas kuma ’yan sanda sun bukaci su da suka tsaya masa su kawo shi.

Yadda abin ya faru a ranar shi ne, Alhaji Musa na tafiya a motarsa ne sai mutanen suka biyoshi suka kara masa mota domin idan ya tsaya su kama shi, shi kuma da zuwa gadar Kawo sai ya fito yana ihu cewa masu garkuwa da mutane za su kama shi.

’Yan kasuwa da sauran mutane masu wucewa kuma da ke wajen sai suka kai masa dauki inda shi kuma ya rika nuna mutane hudun da ke cikin motar da ta biyo shi.

Ganin haka sai matasa suka dirar wa mutanen hudu inda suka fito da diraban motar suka kashe shi nan take tare kuma da kona motar da suke ciki.

Sauran ukun kuma suka nemi tsira da rayukansu, shi kuma mutumin da ya kulla sharrin Alhaji Musa sai aka nemi shi aka rasa domin ya sulale cikin mutane ya gudu abinsa kafin isowar ’yan sanda.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya ce a lokacin da ’yan sanda suka isa wajen sun fahimci akwai ’yan sanda uku da aka aiko daga Jihar Legas domin su taimaka wajen kama wanda ake zargi wanda kuma abokanensa ne da suka yi belinsa a kan wani laifi da ya aikata a Legas.

Kakakin ’yan sanda ya kara da cewa ’yan sandan Legas ne suka nemi sauran mutanen uku wanda sune suka tsaya wa Alhaji Musa har ya samu beli su kawo shi su kuma suka yi bincike har suka gano yana Kaduna shi ne suka zo domin sanar da shi cewa ana da bukatar ganinsa a Abuja.

“Shi kuma daga ganinsu sai ya kwala ihu da sunan wai masu satar mutane ne su. Su kuma mutane da ba su san abin da ke tsakaninsu ba sai suka dirar wa mutanen,” inji shi.

Har ila yau a lokacin wannan hatsaniya mai daukar hoton gidan talebijin na NTA Yunusa Muhammad ya sha da kyar shi ma daga hannun mutasan a lokacin da ya isa wajen.

Ya shaidawa Aminiya cewa Allah ne Ya ceci rayuwarsa domin matasan sun dauki katako sun kai masa doka a kai amma sai katakon ya sauka akan kamararsa.

“Gaskiya Allah ne kawai Ya cece rayuwata domin da wannan katako ya same ni a kai da sai ta Allah. Duk kuwa da rigar da nake sanye da ita na dauke da alamar ni ma’aikacin NTA ne amma duk wannnan bai sa sun daina bugu na ba domin wai duk tare muke da ’yan sanda,” inji shi.

kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna DSP Sabo ya tabbatar da cewa daga bisani ’yan sanda sun bibbiya Alhaji Musa Imam, inda suka samu nasarar kama shi da misalin karfe misalin 5 na yamma a ranar Talata.

Sannan daya daga cikin mutanen da suka samu rauni ya mutu a asibiti, ke nan wadanda suka mutu sun zama uku duk da shi wanda ake kashe bisa zargin cewa mai garkuwa da mutane ne.