✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun nemi Sanata Ahmad Lawan ya amsa kiransu

Wata kungiyar Matasan Jihar Yobe, mai suna ‘Youth Earnestly Ask Senator Ahmad Ibrahim Lawan’ (YEASAIL) da ya amsa kiransu na fitowa takarar kujerar gwaman jihar…

Wata kungiyar Matasan Jihar Yobe, mai suna ‘Youth Earnestly Ask Senator Ahmad Ibrahim Lawan’ (YEASAIL) da ya amsa kiransu na fitowa takarar kujerar gwaman jihar a shekara ta 2019. Matasan sun yunkuro ne suka kafa kungiyar domin yin kira ga shi Sanatan nasu, Sanata Ahmad Lawan, dan Masanin Bade da ya fito takarar gwamna a zabe mai zuwa.

Wannan kira yana dauke ne a wani sako mai dauke da sanya hannun kodinatan su na jihar Yobe, Muhammad Tukur Usman da suka aikewa da Aminiya, inda suke nuni da cewa kokarin sanatan nasu ne na yadda yake musu wakilci na kwarai da taimakawa da yake yi a bangarori daban-daban na yankin da yake wakilta a Jihar Yobe da ma Najeriya baki daya.

Sakon ya kara nuna cewa Sanatan yana bai wa matasan jihar Yobe karfin guiwa shi yasa wannan kungiya ta YEASAIL ta fara yin kira tun yanzu dan ya amince ya amsa kiransu. “Wakilcin Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya wuce iya yankin da yake wakilci na jihar Yobe yana wakilci ne a kasa baki daya” in ji su.

Sun kara da cewa yana bada kulawa sosai a bangaren Ilimi wanda shi ne tushen ci gaban kowacce al’umma kuma Sanata Ahmad yana daukar nauyin dalibai domin yin karatu a ciki da wajen Najeriya, sannan da kokarin sa ne aka samu jami’ar gwamnatin tarayya wacce ake kira da FUGA.

A cewar su yayi kokari wajen inganta kwalejin ilimi dake yankinsa mai suna  Umar  Suleiman college of education Gashua (USCOEGA) ya kuma taimaka wajen samar  da ICT da kuma cibiyar rubuta jarrabawar JAMB, da kuma taimakawa wajen gina islamiyyoyi a cikin kananan hukumomi guda shida da yake wakilta domin kowacce karamar hukuma ta bada waje na musamman ya gina musu azuzuwa tare da bandakuna da kayan ofishi da kuma fanfunan tuka-tuka.

Dadin dadawa, a aikin sa na wakilci, a duk shekara shike lashe kyautar sanatan da yafi kowane sanata aiki da kuma tsayawa akan kare hakkin mutanen sa.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya dauki nauyin (bills) kudurori da yawa wanda suka shafi rayukan mutanen  Najeriya ba iya mutanen da yake wakilta na Yobe kadai ba, misali: Dessert Control Commission Bill, Federal Unibersity Establishment Act.

YEASAIL suka ce da Jajircewansa ne aka canjawa asbitin gwamnatin tarayya dake Nguru waje da kuma taimaka wa asbitin da naurori na tace jini tare da kara samo musu karin kudi daga gwamnatin tarayya da ya kai naira miliyan dari da ashirin. Sannan suka ce Sanata Ahmad Lawan, ya kuma dauki nauyin aikin gyaran ido tare da yiwa masu matsalar idon gilashin su dubu hudu 4000 suka amfana.

Ya kuma sake daukar nauyin tiyatar kaba da aka yiwa sama da mutum dubu uku 3000 a yankin sa na Yobe ta arewa. Bisa ga wannanne suke rokon mutanen Yobe da su taimake su wajen aika sakon ga Sanata Ahmad, tare da sashi ya amsa kiransu domin ya gaji mai girma gwamna Ibrahim Gaidam daga inda ya tsaya.