Da Dumi Dumi

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa

Abba wanda ake zargi

A ranar Asabar, 12 ga Oktoba al’ummar garin Agyaragu-Tasha da ke yankin Jenkwe a Karamar Hukumar Obi a Jihar Nasarawa suka shiga zaman makokin rasuwar wata mai suna Hajiya Zuwaira Audu wacce ake zargin wani dan kishiyarta mai kimanin shekara 30 mai suna Abba Audu da kashe ta.

Wakilinmu ya ziyarci inda lamarin ya auku inda ya gana da kawun wanda ake zargin Malam Suleiman Zakari dangane da lamarin wanda ya ce, “Abin da ya faru shi ne jim kadan bayan mun idar da Sallar Magariba muna zaune muna hira a kofar gidana, sai aka kirani ta waya aka ce Abba ya soki Hajiya Zuwaira wato ita kishiyar mahaifiyarsa da wuka ta rasu. Da jin haka sai muka tashi a guje muka je muka kuma tabbatar da aukuwar lamarin. Daga nan ne sai muka je ofishin ’yan sanda da ke Agyaragu muka sanar da su lamarin. Bayan sun rubuta bayyananmu sai suka hada mu da wadansu jami’ansu suka dauki  hotunan gidan da gawar sai muka dauki gawar muka kai Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya inda bayan an auna gawar an yi komai, da gari ya waye muka sake komawa Lafiya muka dauko gawar muka yi jana’izarta.”

Kan ko ya san dalilin kisan, sai ya ce “A gaskiya binciken da na yi, ’yan uwansa sun bayyana cewa a ’yan kwanakin nan sun lura kamar yaron ba ya da lafiya wato kamar dai yana da tabin hankali. Kuma a cewarsu sun gano haka ne ta halayensa da maganganu marasa ma’ana da yake yi da sauransu. Daga nan sai suka kai shi wani karamin asibiti a Agyaragu da ake kira Moriya Hospital inda aka auna shi sai dai ba a gano ciwon tabin hankalin tare da shi ba. Daga nan sai aka sake kai shi wajen mai maganin gargajiya inda ya tabbatar musu cewa yana da aljanu.

“Mu dai mun dauki lamarin a matsayin kaddara kuma muna yi mata addu’ar Allah Ya jikanta Ya kuma gafarta mata. Don ba ni kadai ba, kusan kowa a yankin nan mamaki yake yi kasancewar Abba mutum ne da tun tasowarsa ba ya da matsala. Bai taba samu rashin jituwa da kowa ba. Kuma akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsa da marigayiyar wace ta rike shi da sauran kannensa tun suna yara bayan mahaifiyarsa ta bar gidan jim kadan bayan rasuwar yayana,” inji shi.

Wakilinmu ya ziyarci Asibitin Moriya inda aka kai Abba don gwada lafiyarsa kuma babban likitan asibitin Mista James Mathew ya ce, “Ba shakka ’yan uwan yaron sun zo da shi nan inda suka ce suna so su tabbatar ko ya kamu da ciwon hauka. Da muka yi gwaje-gwajenmu a karshe aka fito da sakamakon da ya nuna bai da wata matsalar kwakwalwa.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta samu labarin cewa bayan wanda ake zargin ya aikata danyen aikin sai ya gudu ya kai kansa ofishin ’yan sanda da ke kusa da gidan inda aka tsare shi na wani lokaci daga baya aka wuce da shi garin Lafiya inda yanzu yake tsare a Sashin Bincikan Manyan Laifuffuka (CID) na Rundunar ’Yan sandan Jihar.

Kakakin Rundunar, ASP Raman Nansir wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna ci gaba da bincike a kansa kuma da zarar sun kammla za su kai shi kotu don a yi hukunci da ya dace.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya