✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya mutu a lokacin da yake buga kwallo

Wani abu mai kama da almara ya faru a ranar Asabar da ta wuce a kauyen Co Antrim da ke kasar Ailan ta Arewa (Northern…

Marigayi Stuart RossWani abu mai kama da almara ya faru a ranar Asabar da ta wuce a kauyen Co Antrim da ke kasar Ailan ta Arewa (Northern Ireland) bayan da wani matashi dan kimanin shekara 25 mai suna Stuart Ross ya yanke jiki ya fadi kuma nan take ya mutu a lokacin da yake buga kwallo a gasar rukunin ’yan dagaji na kasar da aka fi sani da (Amatuer League).
Al’amarin ya faru ne a lokacin da kulob dinsa Islandmagee II yake karawa da na Belfast’s Shankill United.
An ce a lokacin da wasa ke gudana a minti na 25 sai marigayin ya kamu da ciwon bugun zuciya (heart attack) inda ya fadi kasa sumamme kafin a garzaya da shi asibiti mafi kusa rai ya yi halinsa..
Shugaban kulob din da kuma abokin marigayin mai suna Alan Wilson sun shaidawa jaridar Sunday Life yadda al’amarin ya faru.  Sun ce babu zato ba tsammani  aka ga matashin dan kwallon ya yanke jiki ya fadi a lokacin da wasa ke gudana a daidai minti na 25 kuma hakan ta girigiza daukacin takwarorinsa da ke buga wasa a lokacin inda mafi yawansu suka bar filin cikin gaggawa saboda kaduwa.
Rahoton ya kara da cewa, nan take wasan ya tsaya bayan alkalin wasan da mataimakansa da kuma daukacin ’yan kwallon kowa ya kama gabansa saboda kaduwa.
Shi ma sakataren kulob din Islandmagee ya bayyana cewa za a dauki lokaci mai tsawo kafin sauran matasan ’yan kwallon su cigaba da fafatawa a gasar don da yawa daga cikinsu sun nuna akwai yiwuwar sun daina buga wasan kwallo a rayuwarsu sabili da abin da ya faru da dan uwansu.