✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi fashin jirgi da bindigar roba a Bangladesh

An tabbatar da cewa fasinjan da ya yi garkuwa da mutane tare da barazanar ragargaza jirgin da yake ciki wanda ya tashi daga birnin Dhaka…

An tabbatar da cewa fasinjan da ya yi garkuwa da mutane tare da barazanar ragargaza jirgin da yake ciki wanda ya tashi daga birnin Dhaka a Bangladesh yana dauke ne da bindigar roba

’Yan sanda sun harbe mutumin mai shekara 25 bayan da jirgin ya yi saukar gaggawa.

Mohammad Palash Ahmed da ake zargi

Dukan fasinjojin 148 da ke cikin jirgin na Birman Airlines mai lamba BG147 samfurin 737-800, sun yi ta kansu bayan saukar jirgin a birnin Chittagong.

Daga baya jami’ai sun ce mutumin ba ya da cikakkiyar lafiya kuma ya so ya yi magana da Firayi Ministar Kasar.

A wani aiki da suka kaddamar na tsawon minti 10, dakarun musamman na Bangladesh sun yi dirar mikiya cikin jirgin tare da harbe mutumin, wanda aka ce sunansa Mohammad Palash Ahmed.

Ana fargabar cewa yana dauke da abubuwan fashewa a jirgin mallakin wani kamfanin kasar Dubai, kuma wadansu fasinjoji sun ce sun gan shi dauke da bindiga kamar yadda BBC ya rawaito.

Amma Kwamishinan ’Yan sandan Chittagong, Kusum Dewan a wata sanarwa da ya fitar ya ce mutumin na dauke ne da bindigar roba ta wasan yara kuma ba ya dauke da wani abin fashewa.

Wani kwamandan mai suna Sarwar-e-Zaman, wanda shi ne manajan filin jirgin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa Ahmed ya so ya yi magana da Firayi Ministar Bangladesh, wanda ke ziyara a birnin Chittagong na gabar teku, saboda matsalolin da yake fuskanta a aurensa.

Mista Zaman ya ce: “Dalilan da ya bayar na kwace jirgin su ne cewa wai yana da matsala da matarsa don haka yana son yin magana da Firayi Minista Sheikh Hasina.”

A yanzu masu bincike na kokarin gano yadda har Ahmed ya samu wucewa cikin jirgin da bindigar roba duk da jami’an tsaro da ke wajen.

An kara tsaurara tsaro a filayen jiragen kasar da suka hada da babban filin jirgi na Hazrat Shahjalal International da ke Dhaka sakamakon faruwar wannan lamari.

Jami’an soji sun ce mutumin ya ji rauni sakamakon harbin bindigar da aka yi masa, daga bisani ya mutu.

“Mun yi kokarin kama shi ko ya mika kansa, amma sai ya ki, sai kawai muka harbe shi,” Manjo Janar Motiur Rahman ya shaida wa manema labarai bayan faruwar lamarin.

“Dan Bangladesh ne. Bindigar kadai muka samu a jikinsa,” inji shi.

Ma’aikatan jirgin ne suka nuna damuwa bayan da aka ce mutumin yana nuna wasu alamu na rashin gaskiya da kuma nuna alamar niyyar kwace jirgin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya fada.

Ba a bata lokaci ba wajen zagayewa tare da hana mutane kusantar jirgin bayan saukarsa a filin jirgin Shah Amanat da ke Chittagong, yayin da jami’ai suka yi kokarin yin magana da mutumin.