✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsafa sun yi wa tsohuwa yankan rago

Wata dattijuwa mai shekaru 78 ta gamu da ajalinta bayan wasu da ake zargi matsafa ne sun yi mata yankan rago bayan sun sace ta…

Wata dattijuwa mai shekaru 78 ta gamu da ajalinta bayan wasu da ake zargi matsafa ne sun yi mata yankan rago bayan sun sace ta daga gidanta.

An yi wa dajjituwar mai suna Sabiana Aranilewa yanka ragon ne a garin Ikere-Ekiti, a jihar Ekiti.

Dan marigayiyar mai suna Eyitope Aranilew ya shaida wa manema labarai cewa an nemi mahaifiyar tasa an rasa ne da sanyin safiyar Juma’a, 29 ga watan Mayu bayan ta je wanki a kofar gida.

Ya ce kawar mahaifiyar tasa mai suna Ojolo ce ta ankarar da su bacewar mahaifiyar tasa inda suka bazama neman ta amma ba su gan ta ba sai da yammacin ranar aka gano gawarta yashe a gefen kogi wuyanta a yanke an kuma ciri wasu sassan jikinta.

“Mun sanar wa ‘yan sanda a lokacin da lamarin ya faru. Muna ofishinsu a lokacin da aka sanar da mu cewa an gano gawarta.

“Sun yi mata yankan rago, suka cire wasu sassan jikinta sannan suka jefa gawarta a kogi” inji shi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ekiti, Sunday Abutu ya ce abun takaici ne mai matukar tada hankali, kuma rundunar na bincike domin gano wadanda suka aika ta mummunan laifin.