✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?1

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a…

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Laifin shugabannin kasa ne – Musa Abubakar

Musa Abubakar: “A fahimtata, wannan talaucin da al’ummar kasar nan suke fama da shi, ba laifin kowa ba ne illa rashin adalcin shugabannin kasar nan saboda haka su ne tushen da suka sa talauci ya samu gindin zama a kasar nan, ta hanyar bin guragun dabaru da son rai da rashin hangan nesa, suka zama marasa adalci da yin wasoso da dukiyar kasa, suna boyewa a kasashen waje. Sai uwa uba cin hanci da karbar rashawa amma in ba haka ba, ai kasar nan Allah Ya hore mana komai na arziki da za mu rike kanmu har da sauran makwabta. Rashin samun shugabanni masu adalci da kwatanta gaskiya shi ya maida al’ummar kasar nan tamkar musakai da marayu saboda haka shugabannin gwamnati su ne ummul haba’isin talauta kasar nan.”