✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar talauci da rashin aikin yi a Najeriya: Laifin gwamnati ko na al’umma?5

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a…

Dukkan alkaluman da ake amfani da su na tantance bunkasar tattalin arzikin kasa sun nuna yadda talauci da rashin aikin yi suka yi katutu a Najeriya. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa alhakin kasancewar haka, gwamnati ko al’ummar kasa? Ga ra’ayoyin jama’a, kamar yadda wakilanmu suka kalato mana:

Laifin cin hanci da rashawa ne – Sabo Muhammad

Kwamared Sabo Muhammad: “Ina gani talauci ya samu asali ne sakamakon cin hanci da rashawa da suka yi katutu a zukatan jami’an gwamnati da mutane. Dole sai an samu shugabannin da za su iya gyara wannan matsala kafin mutane su rabu da talauci, ita ma gwamnatin ta samu natsuwa. Saboda ita kanta gwamnatin duk abin da ta mallaka a kullum kirari da talauci take wa kanta balle kuma mutanenta. Kullum ana cewa akwai shirin magance talauci amma cin hanci ya sa ba a gani a kasa. Don haka ina gani laifin gwamnati ya fi yawa saboda ita ke bayar da kudin mutane a yi mata magudin zabe, a lalata akidar talaka da abin da bai taka kara ya karya ba, ya zaba a mured, a hana shi kayan more rayuwa. Shi kuma rashin zuciya ya sa ya yarda da duk abin da ake masa don dan abin da za a ba shi ya sa ya kashe zuciyarsa ya zauna yana jiran ’yan siyasa ko abin da bai taka kara ya karya ba daga gwamnati.”