✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro:Yadda aka kai gawarwakin wadanda aka kashe gidan gwamna da sarki a Katsina

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar jana’izar gawarwakin mutum 18 da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a kauyen `Yar Gamji da ke Karamar Hukumar…

A shekaranjiya Laraba ce aka gudanar jana’izar gawarwakin mutum 18 da ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a kauyen `Yar Gamji da ke Karamar Hukumar Batsari ta jihar Katsina.

An birne gawarwakin ne a makabartar Dan Takum bayan an masu salla a Fadar Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman wanda ya samu halartar Hakimai da wasu masu rike da sarautu tare da jami’an gwamnati da kuma sauran jama’an.

Limamin babban masallacin Katsina, Ustaz Mustapha Ahmed, ne ya jagorancin sallar jana’izar

A ranar Talata ce dai wasu fusatattun matasa suka dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa gidan Gwamnatin Jihar Katsina da Fadar Masarautar Katsina domin nuna rashin jin dadinsu bisa kisan gillar da ’yan bindigar ke musu.

An dai samu rahoton kisan gillar ne a kananan hukomomin Batsari da Jibia da Danmusa da Faskari.

Matasan suna zanga-zangar ce domin rashin dadin yadda jami’an tsaro suka gaza wajen kare du da lafiyarsu, inda suka bayyana cewa ’yan banga da suke yankin sun fi jami’an tsaron amfani.

Aminiya ta gano cewa matsalar ta fara ne a kauyen ’Yar Gamji da ke Karamar Hukumar Batsari, bayan ’yan bindiga sun kashe wasu manoma a lokacin da suke sharar gona.

“A lokacin da suke aiki a gonakinsu, kawai sai ’yan bindigar suka fito a kan babura suka bude musu wuta, inda suka kashe su duka nan take. Sannan kuma daga baya suka shiga cikin kauyen suna harbin kan mai uwa da wabi, inda suke jikkita wasu mutane.”

Mutanen garin sun kara da cewa sun nemi taimakon jami’an tsaro amma babu wanda ya kawo musu dauki.

Jim kadan sai motar ’yan sanda ta shigo kauyen ta kwashe gawarwakin ta kai su Fadar Hakimin Ruma, wanda wannan ne ya fusata matasan kauyen suka fara zanga-zanga.

Daga nan sai matasan suka dunguma suka tafi Ofishin ’Yan Sanda, inda suka samu turjiya daga ’yan sandan wanda hakan ya sa aka harbi matasa uku daga cikinsu.

Harbin matasan ya sa matasan suka kara fusata, wanda hakan ya sa suka debi gawarwakin suka shiga cikin suna zanga-zanga.

Da yake jawabi a kusa Gidan Gwamnati, mai magana da yawun masu zanga-zangar, Aminu Rumah ya ce suna zanga-zangar ce domin su jawo hankalin gwamnati a kan kashe-kashen da ke wakana a yankinsu, da kuma bukatar a kawo musu dauki wajen magance matsalar, inda ya kara da cewa matsalar rashin tsaro ya shafi harkokin noma a yankin, “’yan banga ma sun fi jami’an tsaron tabuka abin a zo a gani. Su jami’an tsaron ba sa zuwa lokacin da muke bukatarsu. Ko yau da muke zanga-zangar ma ’yan sanda sai da suka harbi mutanenmu guda uku.”

Da yake jawabi a game da lamarin, Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnatinsa na matukar damuwa da halin da mutane ke ciki na kashe-kashe, inda ya bukaci mutane su kwantar da hankalinsu domin suna aiki ba dare ba rana wajen magance matsalar.

A nasa jawabin, Sarkin Katsina, Abdulmumini Kabir Usman ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin, sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan mutanen suka rasu.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce, “Da misalin karfe 10 na safe a lokacin da jami’anmu suke amsa kiran mutane, sai ’yan bindiga suka yi amfani da damar wajen kai hari ga manoma a kauyen ’Yar Gamji da ke Karamar Hukumar Batsari, inda suka kashe mutum 18 nan take. Kafin mu kai musu dauki, maharan sun gudu zuwa Dajin Rugu. Mutanen kauyen kuma sai suka fusata, wanda hakan ya suka gudanar da zanga-zangar lumana, yayin da wasu daga cikinsu kuma suka yi niyyar kai wa ofishin ’yan sanda hari.

“Amma an samu zaman lafiya a yankin, domin Kwamishinan ’Yan Sandan Katsina CP Sanusi Buba ya bayar da umarni a tura karin jami’an tsaro zuwa yankin.”