✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maulud: Ayyukan tarzoma ne babban kalubalen musulunci- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce babban abin da musulmi za su yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W.) shi ne su dabbaka…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce babban abin da musulmi za su yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W.) shi ne su dabbaka koyarwarsa a rayuwarsu da zamantakewarsu.

Buhari ya wallafa sakon mauludin ne a shafinsa na Twitter yau Litinin, inda ya ce satar jama’a domin neman kudin fansa da kisan jama’a da yi wa mata auren dole duk sun saba da koyarwar addinin musulunci.

Shugaba Buhari ya ce: “Ina yi wa daukacin musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW. Babbar girmamawa da musulmi za su yi wa Annabi ita ce, dabbaka halayensa na rashin son tayar da zaune tsaye da son zaman lafiya da kuma yin hakuri.”

Buhari, ya kuma kara jan hankalin musulmi da su mayar da hankali wajen yakar akidojin da ke sa tsananin kishin addini da ka iya jefa mutane cikin yanayin ayyukan tarzoma.

Ya kara da cewa “A yanzu haka musulunci na fuskantar barazanar ta’addanci da ake kallon addinin da ita.” A saboda haka ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya kamata wajen kawar da hankalin matasa daga tsaurin addini.

Shugaba Buharin dai ya aike wa ‘yan Najeriya nasa sakon Mauludin ne daga birnin Landan inda yake ziyara, inda kai har zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba sannan ya dawo gida Najeriya.