Search
Subscribe
‘Mawaki Akon zai tsaya takarar Shugaban Amurka’

‘Mawaki Akon zai tsaya takarar Shugaban Amurka’

Fitaccen maqakin nan na Rap a kasar Amurka wanda dan asalin kasar Senegal ne ya bayyana cewa yana tunanin zai tsaya takarar shugabancin kasa a Amurka a zaben 2020.

Jaridar Guardian ce ta ruwaito hakan daga wata tattaunawa da mawakin ya yi da jaridar Newsweek, inda ya ce, “ina tunanin zan tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2020. Amma ba wai kawai ina so in yi takarar ba ne, ina fata mutane za su nuna cewa muna bukatar ka tsaya takara.”

A game da hanyoyin da Trump ya dauka na kasar, Akon cewa ya yi, “Gaskiya ina cikin takaici. Ban jin dadi. Na san lallai akwai fama sosai. Dole zan shirya sosai domin yawancin mutane har da fararen fata ma suna cikin damuwa bisa yadda yake tafiyar da kasar. Amman an gaba akwai sauki.”

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin