✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan Boko Haram sun ranta a na kare a Monguno

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a harin da suka kai da nufin kwace garin Monguno da ke Jihar Borno. Da safiyar Asabar…

Mayakan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu a harin da suka kai da nufin kwace garin Monguno da ke Jihar Borno.

Da safiyar Asabar ne ‘yan Boko Haram suka far wa garin suna harbi kan mai uwa da wabi na sa’o’i suna kokarin kwace garin.

Mayakan na kokarin yi wa garin kawanya ne sojojin Najeriya suka kai wa garin dauki da luguden wuta ta kasa da kuma jirage na tsawon lokaci.

Bayan musayar wutar ne daruruwan ‘yan Monguno suka yi ta murnar yadda sojojin suka fatattaki ‘yan kungiyar da suka jefa garin cikin tashin hankali.

Boko Haram da sojoji na musayar wuta a Borno

Yadda Boko Haram ta zama masana’anta —Ahmad Lawan

Wani jami’in agaji ya ce, “Mun shiga tashin hankali na awanni amma yanzu muna cikin aminci. Mutane sun cika tituna suna murna sojoji sun kora shedanun

“Yanzu kowa na cikin farin ciki an kawo mana dauki kuma sojojin sun kokarta sosai”,  a cewarsa.

Wata majiya tsaro ta ce sojojin sun kora maharan da taimakon luguden bama-bamai da jirage, kuma ana ci gaba da bin sawunsu.
“Komai ya lafa, babu damuwa. An murkushe yunkurin nasu, amma ana bin sawu domin tantance yawan wadanda aka hallaka,” a cewar majiyar.