✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mayakan ISWAP sun kashe sojoji tara a Borno

An yi kare jini biri jini inda sojoji suka kashe mayaka 20, soja 10 suka kwanta dama

Mayakan kungiyar Boko Haram masu mubaya’a ga kungiyar ISIS sun hallaka sojojin Najeriya tara a farmaki da suka kai wa sansanin sojojin a Magumer, Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce mayakan a cikin motocin yaki 10 sun mamaye sansanin sojojin da ke Magumeri a ranar Talata inda a nan dakaru tara suka kwanta dama.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ambato daya majiyar na cewa “’yan ta’addar sun kwace sansanin sojojin ne da misalin karfe hudu na yamma, suka tarwatsa sojojin suka kuma kashe tara daga cikinsu”.

’Yan kungiyar sun kuma kona matoci uku na sojojin ciki har da mota mai sulke da motar haka rami.

Sai dai tawagar sojoji da suka kai wa takwarorinsu dauki sun rutsa ’yan ta’addan suka kuma hallaka 20 daga cikinsu.

Mu muka kaseh sojoji —ISWAP

ISWAP a cikin wata sanarwa ranar Laraba ta dauki alhakin harin na Magumeri amma ta ce soja 10 ta kashe ta kuma kwace motoci da makamai.

Ta yi ikirarin kashe wasu soja 10 a wani hari a garin Baga mai makwabtaka da Tabkin Chadi.

Kungiyar na yawan kai hare-hare a Magumeri a baya-bayan nan inda ta kona asibiti da ofishin karamar hukuma tare da yi wa mazauna kwace.

Tserewar mazauna don gudun hare-haren kungiyar ya sa aka girke sojoji a garin domin samar da tsaro.

Zuwa yanzu sama da mutum 39,000 ne aka kashe a rikicin kungiyar Boko Haram tun bayan bullarta a shekarar 2009.

Rikicin kungiyar da ya raba miliyoyin mutane da muhallansu ya watsu zuwa kasashen Nijar da Chadi da Kamaru, lamarin da ya kai ga kafa rundunar hadin gwiwar kasashen domin murkushe kungiyar.