✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mbappe zai koma Real Madrid a ƙarshen kaka

Idan Modric ya tashi, Mbappe ne zai karbi riga mai lamba 10, irin lambar da yake sa wa a PSG.

Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Kylian Mbappe ya amince zai koma taka leda a Real Madrid idan an kammala kakar bana.

Mbappe mai shekara 25 ya sanar da PSG cewar zai bar kungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni.

Duk da cewa har yanzu Mbappe bai kai ga cimma yarjejeniya ba da Real Maadrid, amma ana sa ran kungiyar za ta sanar da halin da ake ciki nan gaba kaɗan.

Mbappe shi ne kan gaba a ci wa PSG kwallaye, inda yake da 244 a raga, wanda ya lashe kofin duniya a tawagar Faransa a Rasha a 2018.

Mbappe ya bukaci a fayyace makomarsa kafin cikin watan Maris, wanda ya tattauna da shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ranar 13 ga watan Fabrairu da cewar yana son komawa Real Madrid.

Bayan da aka san cewar Mbappe na son barin kungiyar tun ranar Alhamis, hakan ya sa ba a fara saka shi ba a gasar Ligue 1 ranar Asabar a wasa da Nantes.

Daga baya ya shiga karawar, wanda ya ci ƙwallo a bugun fenariti, tuni PSG ta bayar da tazarar maki 14 a kan teburin Ligue 1.

An ce ana sa ran zai amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyar da zai ke karbar £12.8m a kowacce kakar tamaula.

Haka kuma Real Madrid za ta bai wa Mbappe £128m kudin rattaba ƙwantiragi da ladan wasa da sauransu da za a biya cikin shekara tara – sannan zai ke karbar kashi na tallace-tallacensa.

Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya fara tunanin wurin da zai ke saka Mbappe tare da Jude Bellingham da kuma Vinicius Junior.

Idan kuma Luka Modric ya bar Real Madrid a karshen kakar bana, Mbappe ne zai karbi riga mai lamba 10, irin lambar da yake sa wa a PSG.