✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Messi ya zargi Brazil a kan jan katin da ya samu

Shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya zargi kasar Brazil da Hukumar Shirya Gasar Cin Kofin Kudancin Amurka (Copa America)  kan kisisinar da suka shirya…

Shahararren dan kwallon duniya Lionel Messi ya zargi kasar Brazil da Hukumar Shirya Gasar Cin Kofin Kudancin Amurka (Copa America)  kan kisisinar da suka shirya har ya samu jan kati a wasan da Ajantina ta yi da kasar Chile na neman neman matsayi na uku a gasar Copa America.   Ajantina ce ta samu nasara a wasan da ci 2-1.

Sai dai kafin wasan Ajantina ta hadu da Brazil ne a makon jiya a matakin Semi-Fainal inda Brazil ta lallasa ta  da ci 2-0.

Messi ya koka ne  game da yadda aka yi alkalancin wasansu da Brazil da hakan yake ganin wata hanya ce hukumar shirya kwallon ta shirya wa Brazil don ta lashe kofin cikin sauki musamman ganin ana yin gasar ce a kasar Brazil.

“Ina da tabbaci saboda fadin gaskiyar da na yi  game da wasanmu da Brazil ne ya sa aka ba ni jan kati a wasanmu da Chile. Hakan ba zai sa na daina fadin gaskiya ba komai dacinta,” inji Messi lokacin da yake hira da manema labarai.

Wannan shi ne karo na biyu da Messi ya taba samun jan kati a tarihin kwallonsa. Kuma ya same su ne a yayin da yake yi wa Ajantina kwallo ba a kulob din FC Barcelona ba.

Brazil ce ta lashe Copa America a ranar Lahadin da ta wuce bayan ta lallasa Peru a wasan karshe da ci 3-1.

Sai dai tuni Hukumar Kwallon Kafa ta Kudancin Amurka ta kafa kwamitin binciken wannan zargi da Messi ya yi, kuma idan ta gano hakan ba gaskiya ba ce akwai yiwuwar ya fuskanci hukunccin dagewa daga shiga harkar kwallon kafa a nahiyar ciki har da rashin halartar shiga gasar neman zuwa cin Kofin Duniya da Ajantina za ta yi a shekara mai zuwa da kuma gasar cin Kofin Kudancin Amurka.