✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mijina ya yi wa ’ya’yana 3 fyade’

Wata mata mai suna Misis Tope Ogba ta bayyana wa kotun da ke shari’ar matsalolin gida da laifuffukan fyade ta Ikeja a Jihar Legas cewa,…

Wata mata mai suna Misis Tope Ogba ta bayyana wa kotun da ke shari’ar matsalolin gida da laifuffukan fyade ta Ikeja a Jihar Legas cewa, mijinta mai suna Mista Gabriel ya yi wa ’ya’yanta uku fyade.

Alkalin Kotun Mai shari’a Misis K. A. Momoh-Ayokambi ta samu shaidar da ke nuna cewa, mijin Tope ya yi lalata da ’ya’yanta kuma ya yi yunkurin kona ta lokacin da ya samu labarin ta kai shi kara ga hukumomi.

Kotun na tuhumar Gabriel da laifin yi wa ’ya’yan Tope fyade masu shekara 25 da 20 da kuma 13 a gidansu da ke garin Oke-Ogbe a kusa da tashar mota ta Atura a Karamar Hukumar Badagry  a Jihar Legas.

Misis Tope ta bayyana wa kotu cewa, ba ta da  masaniya a kan lalatar da mijinta yake yi da ’ya’yanta a cikin wasu shekaru har sai da karamar cikinsu ta fallasa abin da ke faruwa.

Ta ce: “Ban san abin da ke faruwa ba, sai da na fahimci mijina yana kyarar ’yata ta uku, sannan na fahimci abin da ke faruwa, daga bisani sai na ji jama’ar gari na tsangwamar babbar ’yata a waje. Dana tambayi babbar ’yata a kan jita-jitar da nake ji a gari, da farko sai ta musanta, sai daga baya na san irin tsangwamar da ake wa ’ya’yana daga wajen malamar ’yata ta uku.”

“Da na tuntubi mijina, sai ya ce, kawai an sa wa ’ya’yanmu ido ne, sai na ce masa ba zai yiwu ba a ce kamar karamar yarinya irin wannan ana tuhumarta da aikata irin wannan da mahaifinta,” inji ta.

Misis Tope ta ce, “Tun lokacin da na tunkare shi da wannan magana ban kara samun zaman lafiya a gidan ba, wani lokaci ya da ke ni ya wulakanta ni.”

Misis Tope wadda ’yar kasuwa ce ta bayyana hakan ne lokacin da take cikin damuwa ga hukumar da za ta dauki mataki.

A lokacin da lauyan Mista Gabriel, Mista E. Obelu, ke tambayar Misis Tope ta ce, ba ta san lokacin da mijinta ya fara yin lalata da ’ya’yanta ba. Saboda ita kadai ce, ke ciyar da iyalansu, amma ba ta da wata masaniya game da abin da yake faruwa.

Misis Tope ta ce, ’yarta ta uku mai shekara 13 za ta iya bayar da shaidar abin da ta sani game da mahaifinta.

A lokacin da ’yar Tope mai shekara 13 take zauren kotun da bayyana abin da ta sani game da mahaifinta. Mai shari’a Sururat Soladoye, ta umarci masu sauraren karar  su fice daga zauren saboda shaidar karamar yarinyar.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 7 ga watan Maris, 2019, kamar yadda Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya (NAN) ya sanar.