✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ministan Wasanni zai mayar da ’yar boksin mai  shekara 8  ’yarsa

Ministan Matasa da Wasanni Mista Sunday Dare ya bayyana niyyarsa ta mayar da wata yarinya ’yar shekara 8 mai suna Shekinah da ke wasan damben…

Ministan Matasa da Wasanni Mista Sunday Dare ya bayyana niyyarsa ta mayar da wata yarinya ’yar shekara 8 mai suna Shekinah da ke wasan damben boksin  tamkar ’yarsa.

Ministan ya ce zai dauki nauyinta ne ganin yadda ta kware a damben boksin kuma hakan zai karfafa mata gwiwa wajen yin fice a ciki da wajen kasar nan.

Mista Sunday Dare ya bayyana haka ne a sakon da ya sanya a shafin sadawarsa na Twitter a ranar Litinin da ta gabata.  Sakon yana kunshe ne hade da wani faifan bidiyo inda aka ga Shekinah tana samun horo daga wajen kocinta a Jihar Legas.

Ganin yadda yarinyar ta kware wajen wasan damben boksin ne ya ba Ministan sha’awa inda ya yanke shawarar daukar nauyinta ya mayar da ita tamkar ’yarsa.

Jim kadan bayan Ministan ya bayyana wannan kudiri ne sai jama’a suka shiga  tofa albarkacin bakinsu wajen yaba wa Ministan game da wannan kudiri da yake da shi na daukar nauyin Shekinah. Sai dai sun nemi Ministan ya karkata akalarsa wajen zakulo hazikan matasa a bangarorin wasanni daban-daban kamar yadda ya yi a kan Shekinah.

Idan za a tuna jim kadan bayan an rantsar da Sunday Dare a matsayin Ministan Wasanni ya yi alkawarin bullo da shirin zakulo matasan ’yan wasa daga kowane sashe na kasar nan da ake kira Hunt Talent Programme (HTP).

Yanzu dai za a iya cewa Ministan ya fara cika alkwarin ne bayan ya zakulo Shekinah ’yar shekara 8 mai wasan damben boksin.