✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Modric yana son barin Madrid

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna yadda dan kwallon tsakiya Luka Modric ya fara yunkurin barin kulob din…

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din Real Madrid na Sifen sun nuna yadda dan kwallon tsakiya Luka Modric ya fara yunkurin barin kulob din a karshen kakar wasa ta bana, inda tuni ya dauki hayar shahararren dillalin da ke sayar da ’yan kwallo Jorge Mendes don ya tsara cinikin sayar da shi.

Modric, wanda yake rike da kambun Gwarzon Dan Kwallon Duniya, tun a bara kulob din Inter Milan na Italiya yake zawarcinsa inda ya yi masa tayin kwantaragin shekara 4 kan albashin Yuro miliyan 9 duk shekara (kimanin Naira biliyan 37 da miliyan 350).

Sai dai jaridar Mediaset ta ruwaito cewa Modric ya fi sha’awar ya koma kulob din Jubentus na Italiya maimakon Inter Milan inda yake sha’awar sake haduwa da Cristiano Ronaldo wanda suka taba yin yi kwallo tare a kulob din Madrid.

Yanzu haka Modrid yana da shekara 33 da hakan ya nuna ya fara tsufa a wasan kwallon kafa.