Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mota ta hallaka almajirai 13 a Jihar Taraba

Al’ummar karamar Hukumar Gassol da ke Jihar Taraba sun shiga juyayi da rudani sakamakon hallaka almajirai 13 ’yan kasa da shekara 15 da wata motar daukar fasinja mallakar kamfanin sufuri na Jihar Adamawa  ta kashe a kauyen  Gorundo da ke yankin Gunduma a karamar hukumar.
Wakilinmu ya jiwo daga yankin cewa almajiran sun tafi wani karamin tafki ne da ke dab da bakin babbar hanyar Jalingo zuwa Wukari suna wanka lokacin da hadarin ya auku.
Wani almajiri da ya tsira daga hadarin mai suna Muhammadu Abdulkarim mai shekara 13 ya shaida wa wakilinmu cewa suna zaune a bakin kwalbati wasu daga cikinsu suna wanka a cikin tafkin sai ya ji karar wata mota ta nufo inda suke. Ya ce jin karar motar sai ya fita da gudu a firgice  wasu kuma suka fada cikin tafkin amma sai motar ta fada  cikin tafkin ta  take wasu almajiran suka rasu.
Ya ce, motar ta kuma haura ta sake take wasu almajiran da ke gudun tsira.
Muhammadu Abdulkarim ya ce motar ta buge shi ta jifar gefe, “Kuma da na tashi sai na ga dan uwana a mace na kama kuka na nufi makarantar allonmu na shaida wa malaminmu abin da ya faru,” inji shi.
Ya ce su 13 ne iyayensu suka turo su karantun allo daga garin Baladde da ke karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi kuma wadanda motar ta kashe duk ’yan uwansa ne daga garin nasu.
Abdulkarim ya ce a yanzu hankalinsa a tashe yake saboda rasuwar ’yan uwansa da kullum suke tare suna karatu. “Ina son a koma da ni garinmu wajen iyayena in zauna can in ci gaba da karatu,” inji shi.
Malamin almajiran Malam Usman ya shaida wa wakilinmu cewa wannan lamari ya sa daukacin jama’ar Gunduma da na karamar Hukumar Gassol  cikin rudani da juyayi. Ya ce yana zaune a makaranta wani almajirinsa ya zo a guje ya fada masa cewa wata mota ta kashe ’yan uwansa masu yawa shi ma da kyar ya tsira.
Malam Usman ya ce da jin haka sai ya yi maza ya sanar da  jama’a abin da ya auku, inda daukacin jama’ar garin suka fitio suka tafi inda hadari ya auku. Ya ce da isarsu wurin ke da wuya suka barke da kuka wasu na salati saboda ganin yadda motar ta yi kaca-kaca da almajiran wasu ta yi rugu-rugu da jikinsu sai jini ke fita. “Nan take muka hada gawarwakin yara 13 kuma wasu biyar da suka ji munanan raunuka aka  kai su asibitin Jalingo don yi musu jinya,” inji malamin.
Malam Usman ya ce a cikin almajiran da motar ta hallaka akwai dansa mai suna Zakariya’u Usman, kuma akwai wasu almajirai daga wasu makarantun allo biyu da ke garin Gunduuma kuma tuni  suka shaida wa iyayensu aukuwar hadarin.
Ya ce tunda yake karantar da almajirai bai taba ganin tashin hankali irin wannan ba. Ya ce sun tambayi direban motar yadda hadarin ya auku amma ya ce shi ma bai san yadda abin ya auku ba.
Da yake magana kan hadarin Hakimin Gunduma, Wali Adamu Umar ya bayyana wa wakilinmu cewa hadarin ya tayar da hankalin jama’ar yankinsa da na karamar hukumar da jihar.
Wali Adamu Umar ya ce duk da yake da yawa daga cikin almajiran sun fito ne daga wasu garuruwa neman ilimi a garin na Gunduma  amma akasarin jama’ar garin sun saba da su, inda rasuwar wadannan yara kanana ta haifar da juyayi da tausayi da rudani.
Ya ce yau shekara 10 da aukuwar wani hadari da ’yan fashi da makami suka haifar da ta jawo mutuwar wadansu ’yan kasuwar karamar hukumar 12 a kusa da inda motar ta kashe yaran, bayan da ’yan fashin suka tsare hanya suka tilasta wa ’yan kasuwar kwantawa a gefen hanyar wata safa ta zo ta bi ta kansu.
Ya ce Gwamnan Jihar Darius Ishaku ya aiko da tawaga a karkashin Sakataren Gwamnatin Jihar don yi wa jama’ar garin ta’aziyyar rashin da aka yi, inda gwamnantin ta nuna matukar juyayi da tausayi kan rasuwar yaran da Allah kadai Ya san irin gudunmawar da za su iya bayarwa ga kasar nan da Allah Ya ba su tsawon rai. Ya ce gwamnantin ta bayar da taimakon Naira miliyan daya kuma ta dauki nauyin biyan kudin jinyar sauran yara biyar da suka suke kwance a babban asibitin Jalingo.
Wali Umar ya ce Shugaban karamar Hukumar Gassol Alhaji  Tukura Bashiru ya zo da jami’an karamar hukumar sun yi ta’aziya .
Har zuwa hada wannan rahoto kamfanin da ya mallaki motar da ta hallaka yaran bai bayar da taimakon ko sisin kwabo ba, kuma Aminiya ta gano kamfanin yana kokarin ’yan sanda su bayar da belin direban nasu.

ADVERTISEMENT