✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho ya kwace Mataimakin Kyaftin a wajen Pogba

Kocin Manchester United na Ingila Jose Mourinho a ranar Talatar da ta  wuce ne ya fada wa dan kwallonsa Paul Pogba cewa daga ranar ba…

Kocin Manchester United na Ingila Jose Mourinho a ranar Talatar da ta  wuce ne ya fada wa dan kwallonsa Paul Pogba cewa daga ranar ba zai sake amincewa dan kwallon ya sake zama Mataimakin Kyaftin ba, a duk lokacin da ainihin kyaftin Antonio balencia ba ya cikin wasa.  Tuni kocin ya maye gurbin Pobga da Ashley Young.

Kocin ya harzuka ne saboda wadansu kalamai da Paul Pogba ya yi jim kadan bayan wasan United da Wolbes a gasar firimiyar Ingila a ranar Asabar da ta wuce, bayan an tashi wasan kunnen doki da ci 1-1.

A hira da manema labarai Pogba ya soki dabarar da kocin yake amfani da ita wajen sanya su buga wasa a fili, da a ganinsa hakan ne ke kawo wa ’yan kwallon matsala inda ba su iya tabuba abin kirki.  Pogba ya shawarci kocin ya rika amfani da dabarun kai hari ba mayar da hankali wajen tare baya (defense) ba.

Yanzu dai ana ganin dangantaka ta yi tsami a tsakanin Pogba da kocin, al’amarin da ake ganin ba zai haifarwa kulob din da mai ido ba, duk da kocin ya musanta wannan zargi.

A ranar Talatar da ta wuce ma kulob din Derby County ya fitar da na United a gasar cin kofin English League Cup (ELC) a bugun fanariti, bayan an tashi wasa da ci 2-2.  Wannan sakamako ya kara jefa Mourinho cikin kangi inda yake shan suka daga wajen magoya bayan kulob din a sassan duniya.