✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun gina masallatan Juma’a sama da 100 a Najeriya – Dokta Muhyideen

Daraktan Cibiyar Yada Ilmi ta Al-Hufaazh da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, Dokta Muhyideen Ibrahim Solahuddeen ya bayyana cewa ya zuwa yanzu, cibiyar ta…

Daraktan Cibiyar Yada Ilmi ta Al-Hufaazh da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna, Dokta Muhyideen Ibrahim Solahuddeen ya bayyana cewa ya zuwa yanzu, cibiyar ta gina masallatan juma’a sama da guda 100 a jihohi daban daban a Najeriya. Dokta Muhyideen Ibrahim ya bayyan haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen bude wani sabon Masallacin Juma’a da cibiyar ta gina, a Makarantar Nurudeen da ke Unguwar Laranto a garin Jos, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce sun gina wadannan masallatai ne a jihohin Kaduna da Oyo da Kogi da Zamfara da Kano da kuma Filato.

Har’ila yau ya ce cibiyar ta gina makarantu da dama a wurere daban daban na Najeriya. Ya ce babban burin wannan cibiyar shi ne ta kafa jami’a a Najeriya.

Dokta Muhyideen ya yi bayanin cewa babban abin da ya karfafa masu gwiwar gina wannan sabon masallacin juma’a  a wannan tsohuwar makaranta da ta shekara 70 da kafuwa shi ne ganin yadda babu masallaci a makarantar.

“Za a rika yin sallar juma’a  da sauran karatuttukan addinin musulunci. Kuma muna da niyyar mu kafa makarantar Haddar Alkura’ani a wannan makaranta.”

Da yake jawabi lokacin da yake karbar makullan sabon masallacin, Sakataren Gudanarwa na kungiyar Jama’atu Nasril Islam, Sheikh Abdul’azeez Yusuf  ya yabawa cibiyar kan gina masallacin.

Ya yi kira ga al’ummar musulmi su yi kokari suna bada gudunmawarsu wajen yada addinin musulunci.

Ya ce gina masallaci yana da matukar mahimmanci, domin yana daya daga cikin sadakatur jariya.

Sannan ya yi kira ga makotan masallacin da su yi kokarin raya masallaci, wajen yin salloli tare da yin karatuttukan addinin musulunci.