Da Dumi Dumi

Mun yi murnar ranar ’yancin ’yan jarida ta duniya

Ko shakka babu da bazarku muke taka rawa, domin kuwa bikin farar kaza su balbela ba gayyarsu ake ba.  Ina amfani da wannan damar da taya duk wani dan jarida murnar wannan rana da fatar za a kara zage damtse da ayyuka nagari, kowa ya ga yadda kuka ba da gudunmawa wajen tabbatar da ayyukan ku cikin gaskiya da kwatatanta adalci, musamman a yankunan mu na Najeriya da Nijar , inda kuka taka rawa wajen fadakar da al’ummar mu.  Domin samun nasarar yin Babban Zabe a Najeriya da Nijar cikin kwanciyar hankali da lumana, uwa uba kuma yadda kuka tabbatar da wayar da kan jama’armu a kan cutar lasa da ta so yi mana kutsen burgu a Afirka. Hakika mun yi jinjina ga duk ’yan jaridar cikin gida da waje, musamman yadda ake samun ci gaba da nasarar ayyukan ku.
Kana a gefe daya ba zan manta da cin zarafin ‘yan jaridar da muke ganin wasu na yi ba, saboda fede biri da gaskiya da suke yi. Tabbas kamar wakilan Rediyo France International da kasar Kamaru jami’an tsaro suka kama, har ta kai an fara shari’a da kuma wani wakilin BBC da muke ji an kama a Jamhuriyar Chadi.
Don haka muke kira da Gwamnatocinmu na Afrika su sani cewa, dole ne a ce da mijin iya Baba; dole ne a yi gaskiya; dole ne kuma a fadeta. Kamen ’yan jarida da cin zarafinsu sam ba abu ne da ya kamata a lamunta ba. Duk kasashen da suka ci gaba, sun ci gaba ta hanyar yada manufofin su na gaskiya da zahiri ya zama wajibi matukar dan jarida bai taka dokar yada labarai ba, ba dalilin garkame wani a bakin aikinsa ba, saboda manufarku ta siyasa.
A karshe ina kira ga ’yan uwa, ’yan jarida da su kara ba da himma in dai akan kiyaye dokokin aikisu ne, su tabbatar da bin doka da oda da samun sahihin labari don ciyar da nahiyarmu ta Afirka gaba. .Kana dole fa dan jarida ya zama mai bin tsarin zamani matukar yana son aikinsa ya inganta.
Abin bakin ciki fa kana iya cin karo da dan jaridar da ko akwatin i-mail na sadarwa ba shi da shi, musamman kafofin sadarwa nan na zamani ya zama lallai dan jarida ya rika bibiyar su, don tabbatar da tace jita-jita da gaskiya komai dacinta, da kauce wa fadawa tarkon ’yan siyasar mu na zamani masu kin gaskiya don neman saka yankunan mu cikin wani yanayi. Wassalam na gode
Hafizu_Balarabe_Gusau
07035304499.

Share