✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna goyon bayan ‘Sabuwar PDP’ – Kwankwasiyya

kungiyar PDP Kwankwasiya  ta  sha alwashin goya wa Sabuwar PDP baya dari bisa dari. Sakataren kungiyar kuma Mashawarcin Gwamnan Jihar Kano kan Al’amuran Watsa Labarai,…

kungiyar PDP Kwankwasiya  ta  sha alwashin goya wa Sabuwar PDP baya dari bisa dari. Sakataren kungiyar kuma Mashawarcin Gwamnan Jihar Kano kan Al’amuran Watsa Labarai, Sharu Garba Gwammaja ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano.
Malam Sharu Garba ya ce Sabuwar PDP wata hanya ce dodar da za ta kai talakan kasar nan ga cin ribar dimokuradiyya, don haka ya nemi jama’a a su ba shugabannin Sabuwar PDP hadin kai da goyon baya.
“Babu shakka wannan hanya ce mai bullewa ga talakan kasar nan, dubi ga irin zaratan mutane masu kishin kasa da suke tare da ita wadanda dukkansu mutane ne da ke son ci gaban talaka da dorewar dimkuradiyya a kasar nan,” inji shi.
Ya ce ba sa shakkun karbuwarta a kasa ganin irin dimbin manyan mutanen da ta tara irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnoni irin su Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da dimbin sanatoci da ’yan majalisar wakilai.
A nasa jawabin wakilin dattawan kungiyar Alhaji Gambo dampass ya yi kira ga jama’ar kasar nan musamamn ’ya’yan Jam’iyyar PDP su fito su mara wa wannan tafiya baya, domin a kai ga nasara. “Ya kamata jama’a su fahimci cewa wannan ba wata sabuwar jam’iyya ce ba, a’a Jam’iyyar PDP ce wacce aka saba da ita, sai dai samun gyara da aka yi a ciki. Don haka ga ’ya’yan Jam’iyyar PDP musamman mabiya Kwankwasiyya su sani ga dama ta samu wacce za su nuna wa Gwamna irin kaunar da suke yi masa ta hanyar nuna goyon bayansu ga wannan tafiya,” inji shi.    
Shi kuwa Alhaji Salisu Ayo Gawuna wani na hannun daman Gwamna Kwankwaso ya ce Mutanen da suka kafa Sabuwar PDP sun yi haka ne ba don amfanin kansu ba, sai don ceto talakan kasar nan daga fadawa halin kaka-ni-ka-yi.