✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna tattaunawa kan fara aiki da tsarin 5G – Sunday Dare

Mista Sunday Dare, Shi ne Babban Kwamishina na Tattala Masu Ruwa da Tsaki na Hukumar Sadarwa ta NCC. A wannan tattaunawar ya yi magana kan…

Mista Sunday Dare, Shi ne Babban Kwamishina na Tattala Masu Ruwa da Tsaki na Hukumar Sadarwa ta NCC. A wannan tattaunawar ya yi magana kan batutuwan da ke gudana a masana’antar tarho:

Shin da gaske Najeriya ta cimma kashi 30 cikin 100 na amfani da Intanet?

Eh, mun cimma haka shi ya sa muka fitar da kididdiga don kowa ya gani kuma ya lissafa. Wadanda suke cewa ba mu cimma burin ba suna amfani da tsohon rahoto ne na kungiyar kasa da kasa kan harkokin tarho sun manta cewa Hukumar NCC ce ta samar da kididdigar da Kungiyar ITU ke amfani da ita. Mu ne masu ajiyar kiddigar bayanai kuma muna da kwarewa ta musamman kan aunawa. Idan aka yi la’akari da kididdiga ta ainihi mun cimma burin har ma mun wuce shi. Abin sha’awa ma shi ne babu wanda ya yi inkarin kididdigarmu wacce ta sanya alamar tambaya kan manufar wadanda suke cewa ba mu cimma burin ba.

Me ya sa Hukumar NCC ta fi damuwa da batun Intanet ’yar yawo ba ta damuwa da samar da wadda ba ta tafi-da-gidanka ba?

Da farko mutanen da suka san batun sosai suna nuna kamar cewa hakan wata alama ce ta yin watsi da tsarin samar da Intanet wanda ba na tafi-da-gidanka ba. Wannan rashin adalci ne  kuma ba gaskiya ba ne. Ko dai sun yi wa lamarin mummunar fahimta ko suna sane. Gaskiyar ita ce tsarin samar da Intanet na kasa yana tafiya ne da tsarin tafi-da-gidanka da kuma wanda ba na tafi-da-gidanka ba kuma Hukumar NCC tana aiki a kan dukkan biyu.

Shi tsarin samar da Intanet da ba na tafi-da-gidanka ba yana bukatar ka sanya wayoyi a kasa. Kuma yin haka na bukatar ka samu amincewa daga gwamnatocin jihohi. Shekaru masu yawa masana’antar tana fama da yawan haraji da tsaikon samun amincewar da lalata wayoyin da aka sanya yayin ayyukan hanyoyi da umarnin tsayar da aiki ba gaira- babu dalili da sauransu. Wani tsohon Minista ya taba cewa fiye da rabin kudin da ake kashewa wajen sanya layuka a kasa na tafiya ne a biyan haraji. Idan batun ya ci gaba da kazanta to ba a tallafa wa masu zuba jari ba.

Me kuke yi a kan wannan batu? Hukumar NCC ba ta zauna tana kallo ba. Baya ga tuntubar gwanatocin jihohi ta hanyar Hukumar Gudanarwa da Kungiyar Gwamnoni da makamantansu, mun shiga cikin batun ta hanyar yi wa kamfanonin Infracos su samar da kafar sadarwa wacce za ta bai wa kowa dama. Mun samar musu da ragi mai rahusa don saukaka kudin da za su kashe. Muna sa ran hakan zai fara samar da sakamako gamshashshe amma babban al’amarin shi ne samun goyon bayan gwamnonin jihohi. Hakan yana da matukar muhimmanci. Najeriya kasa ce mai  jihohi 36 ba za mu gaya masu kudin da za su karba ba na sanya wayoyi sai dai mu roke su muna sa ran za su ga alfanun abin na tsawon lokaci na zamar da jihohinsu masu dauke da kayayyakin sadarwar tarho.

Daya daga cikin muhimmin hanyoyin kare kayayyakin sadarwa shi ne yadda muke neman a cire shinge sanya wayoyi da majalisun dokoki suka sa, kudirin dokar yana gaban Majalisar Dokoki ta Kasa ’yan shekarun nan, muna sa ran za su yi aiki a kan kudirin dokar na ba da dadewa ba. Hukumar NCC ta yi aiki tukuru kan kudirin dokar.

Mene ne ainihin abin da Hukumar NCC take nufi da rajistar layi karo na biyu, me ya kunsa?

Yayin da muke bin diddigi kamar yadda Shugaban Hukumar NCC ya yi magana a kai, muna aiki kafada-da-kafada da Hukumar Yin Rajistar Katin Zama Dan Kasa (NIMC) don hada katin dan kasa da bayanan rajistar layi. Nan kusa za ka iya rajistar layinka ta hanyar nuna lambarka ta dan kasa hakazalika lambar layinka.

Hakan na nufin za a samar da rajistar layi da ta zama dan kasa daya. Hakan yana bukatar sanya ido da tsare-tsare da kuma gyare-gyare amma muna kan hanya.  Kamar Shugaban Hukumar NCC ya ce, abin da ake son cimmawa shi ne tabbatar da samar da ma’adanar kididdiga wacce jami’an tsaro da sauran hukumomi za su dogara da ita kamar yadda ke faruwa a wasu kasashe. Muna amfani da tsari mafi cancanta kuma muna da kwarin gwiwar za mu samu nasara.

An ce Najeriya ba ta shirya fara tsarin Intanet na 5G ba. Me Hukumar NCC take yi kan wannan batu?

Watanni kadan da suka gabata mun yi taro kan shirya fara amfani da tsarin 5G inda dukkan masu ruwa-da-tsaki suka tattauna tsarin shari’a da sanya ido da batutuwan kimiyya, muna tsara hanyar da za a yi amfani da ita. A ce wai Hukumar NCC ba ta sanya masana’antar ta shirya ba ya zama ko dai rashin sani ko ganganci.

Dadin dadawa kan batun tsarin 5G mun bude tattaunawa da tuntuba kan wani tsari don yin amfani da jirage marasa matuka da makamantansu. Mun zama jagora kan tattaunawa kan samar da sababbin dabarun kimiyya da kere-kere. Wannan shi ne abin da muke yi koyaushe.

Kwanakin baya Hukumar NCC ta shelanta yin gyara kan kididdigar yawan masu amfani da layin waya wanda ya nuna raguwa daga kashi 123 cikin 100 zuwa kashi 91 cikin 100 da aka ce an cimma. Amma wasu kwararru sun aibata wannan sabuwar kididdigar. Sun ce idan aka yi la’akari da mallakar layi fiye da daya a waya daya lambar ta yi kasa sosai. Sun yi ikirarin cewa akwai fiye da ’yan Najeriya miliyan 30 da ba su taba ganin salula ba. Me za ka ce kan wannan?

Hukumar NCC hukuma ce mai dogaro da kididdiga dukkan kididdigar an wallafa ta a shafinmu na yanar gizo don kowa ya gani. Kan batun ’yan Najeriya miliyan 30 da ba su taba ganin salula ba, gaskiyar ita ce shekaru da suka gabata Hukumar NCC ta gano garuruwa 200 da ba su da layin waya kuma tuni aka fara aiki tare da hadin kan kamfanonin tarho don cike wannan gibi. Abin da muke yi shi ne mu ga mun samar wa wadannan garuruwa tsarin layi na 2G mu ga yadda za mu samar musu  Intanet da za su iya yin amfani da shi cikin rahusa. A yanzu mun ce yawan al’ummar wadannan garuruwa ya kai miliyan 35. Ba wai wadannan mutane ba su taba ganin wayar salula ba, ba su da layi ne. Ka fassara wannan da cewa mutum miliyan 35 ba su taba ganin wayar salula ba zarmewa ce.

Gaskiya ce Najeriya ita ke da yawan masu amfani da layukan waya fiye da daya. Hakan yana daga cikin alfanun samar da kasuwa mai bayar da damar gasa. Mutane suna da matukar lura da farashi saboda haka yin amfani da layi fiye da daya zai ba su damar komawa kan tsarin wani layi cikin sauki inda kwalliya za ta biya kudin sabulu.. Mun san haka sosai shi ya sa muka tabbatar da kididdigar masu amfani da yanar gizo. Tsarin teledensity shi ne tsarin da aka amince da shi a duniya na gano yawan masu amfani da yanar gizo shi ne muka yi amfani da shi.

Wane mataki kuke dauka kan haraji iri-iri musamman kan batun Hukumar NCAA?

Kan batun Hukumar NCAA, mun yi murna Hukumar NCAA ta janye barazanar da ta yi. Amma don mu kara bayyana game da muhimmancin Hukumar NCAA na kare sararin samaniyar Najeriya kuma hakan yana da kyau. Batun sufurin jiragen sama batu ne da ya shafe mu. Muna tambaya ko akwai wata hanya mafificiya  ta tunkarar batutuwa da suka fi  barazanar rushe kayayyakin kasa wadanda za su yi tasiri marar kyau kan tsaron kasa da walwala da kuma tattalin arziki. Saboda haka za mu ci gaba da tafiya da masu ruwa-da-tsaki don ganin an kauce wa wannan batu nan gaba.

Batun rajistar layi ba bisa ka’ida ba na tayar da kura a’ yan kwanakin nan a masana’antar, mene ne ainihin abin da ya faru?

Ana aiki tukuru don a daidaita bayanan Hukumar NIMC kuma muna yunkurin ganin nan gaba idan kana da lambar dan kasa ba sai ka bi doguwar hanyar rajista ba. Ya zama wajibi a hada kai don a cimma wannan batu.

Wane mataki Hukumar NCC take dauka don tafiya kafada-da-kafada da masu ruwa- da-tsaki?

Hukumar NCC ta dukufa ka’in-da-na’in wajen samar da tuntuba kan duk wata shawara da za ta yanke. Muna da tsari mafi dadewa na yadda za a gana wacce ta kunshi ganawa daban-daban da yadda ake yin dokoki da za su karfafa masu ruwa-da-tsaki su yi amfani da hakan.