Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Muna zinace-zinace da shan kwayoyi da sunan jihadi – Tubabben dan Boko Haram

Shugaban Vangaren Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Vangaren Boko Haram Abubakar Shekau

Wani tubabben dan Boko Haram ya bayyana yadda aka yaudare su da sunan jihadi aka jefa su cikin bala’i.

Kungiyar Boko Haram dai ta ja hankulan dubban matasa domin shiga cikinta, yayin da ta tilasta wa wadansu dubbai ta hanyar sacewa da yi musu barazanar kisa matukar suka yi kokarin ficewa daga cikinta.

ADVERTISEMENT

Wani matashi da ya tuba, ya ce da farko rashin aikin yi ne ya ja hankalinsa har ya shiga kungiyar Boko Haram.

“Sun yaudare mu ne da sunan Musulunci. Kuma da muka duba muka gani sai muka ga ba Musulunci ba ne, illa dai yaudara.” A cewar matashin da ya tuba din kamar yadda ya shaida wa BBC.

ADVERTISEMENT

Ya ce a lokacin da suka shiga sun ga wani abokinsu yana zuwa da kudi, yayin da su kuma suke fafutikar neman aikin da za su rika yi su samu kudi.

Ya kara da cewa abokin nasu ya fara jan wasu daga cikinsu, inda a farko ake biyansu Naira 3,000 a duk lokacin da suka kai hari, ko suka kwato kudi ko kuma aka biya su kudin fansar satar mutum.

Daga baya kuma ya ce sun koma daji inda ake tura su leken asiri da kuma tattara bayanai a wajen da ake so a kai hari.

Ya ce a lokacin abin da ake ba su bai wuce Naira 3,000 ba, kuma za a ce akwai manya wadanda za su zo su ba su Naira dubu 500 ko dubu 600.

Sai dai ya ce har ya fita daga kungiyar bai taba ganin wani babba a kungiyar ba, in dai ba wadansu da za su zo da manyan bindigogi su ba su ba a wasu lokutan.

Matashin wanda ya shafe shekara takwas tare da Boko Haram, ya ce da farko yana jin dadin cewa addinin Musulunci yake yi wa aiki. Amma daga baya da ya gano cewa kungiyar ta kauce wa addinin Musulunci ya shiga damuwa sosai.

“Ga Kur’ani a ajiye, na duba na ga Allah Ya hana zina, ya hana shaye-shaye, sai na ga cewa ga kwayoyin, ga zinar, a kamo mata a zo a yi ta zina da su, wani ma bai damu da Sallah ba kuma za a zo a kashe wanda yake Sallar,” inji shi.

Ya ce shi ya sa suka yanke hukuncin cewa ba don Allah ake wannan abin ba. Kuma suka yanke shawarar fita daga kungiyar.

Ya ce kungiyar tana tura mutane kasuwanni da kauyuka domin leken asiri da tattara bayanai da kuma nazartar yadda yanayin tsaro yake.

Matashin ya ce babban abin da yake nadama a kasancewarsa dan Boko Haram shi ne kashe wani tsoho da ya yi yayin da suka kai hari a kauyen Gajaganna.

Ya ce bisa kuskure ya harbi tsohon, kasancewar a lokacin bai iya rike bindiga ba. Ya ce duk lokacin da ya tuna hankalinsa yana tashi, kuma a wasu lokutan idan ya rufe ido sai ya rika ganin tamkar tsohon yake dawo masa.

A kimanin shekara takwas da ya shafe tare da ’yan Boko Haram ya ce bai taba ganin shugaban kungiyar Abubakar Shekau ba, ko wadansu manya na kusa da shi.

Ya ce da dama daga cikinsu sun rika fatar yin arba da Shekau din su kashe shi, saboda irin zaluncin da ya ce ake yi musu.

A cikin dajin dai ba a ba su kudi, kuma ba a barinsu su shiga gari, sai dai idan za a tura su leken asiri.

Daga karshe matashin tare da wadansu takwarorinsa 20 sun yanke shawarar barin kungiyar, bayan da suka gaji da kuncin rayuwa da suke fuskanta. Sannan suka mika kansu ga sojojin Najeriya, inda daga baya aka koyar da su sana’o’i.

A yanzu matashin ya koyi sana’ar kafinta, kuma ya ce rayuwarsa ta inganta, domin yana yin aiki ana biyansa, kuma yana samun karbuwa a sana’ar ta sa.