Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mutum 15 sun mutu a hadarin mota a Ekiti

Akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya faru a daren ranar Asabar a garin Iworoko Ekiti kusa da Ado Ekiti babban birnin jihar Ekiti.

Majiyar Kamfanin dillancin labarai NAN ta ce, hadarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren Asabar  lokacin da wata babbar motar daukan kaya dauke da shinkafa ta kauce hanya ta yi cikin babbar kasuwar garin.

ADVERTISEMENT

Wani ganau ya ce, motar afkawa shaguna uku da kuma wata motar fasinja kirar bas makare da fasinjoji a ciki.

ADVERTISEMENT