✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun mutu, 5 sun nutse a hadarin jirgin ruwa a Legas

An tabbatar da rasuwar mutum uku a jirgin ruwa da ya dauki fasinjoji 20 a  tsakanin gadar Liverpool da Coconut da ke jihar Legas. Janar…

An tabbatar da rasuwar mutum uku a jirgin ruwa da ya dauki fasinjoji 20 a  tsakanin gadar Liverpool da Coconut da ke jihar Legas.

Janar Manaja na hukumar bayar da agaji (LASEMA), Mista Adesina Tiamiyu ya tabbatar da aukuwar lamarin da ya faru ranar Laraba da misalin karfe 8:20 na dare.

Tiamiyu ya ce, fasinjoji biyar sun bace yayin da hukumar ta kubutar da mutum 12.