✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3000 sun amfana da shirin maganin ido kyauta a Kano

Akalla mutum dubu uku ne a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa suka amfana da shirin kula da lafiyar idanu kyauta da dan majalisa mai…

Akalla mutum dubu uku ne a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa suka amfana da shirin kula da lafiyar idanu kyauta da dan majalisa mai wakiltar yankunan a Majalisar Wakilai ya shirya tare da hadin gwiwar Asibituin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

An dauki tsawon kwana uku ana gudanar da shirin wanda aka yi shi a Babban Asibitin Dawakin Kudu.

A zantawarsa da manema labarai dan majalisar Alhaji Mustapha Bala Dawaki ya ce  shirin wanda aka ware wa Naira miliyan 50 don gudanar da shi an shirya shi ne don amfanin mutanen yankin  a karkashin ayyukan mazabu na shekarar 2019.

A jawabin shugaban shirin wanda kuma shi ne Shugaban Sashen kula da Lafiyar Idanu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Dokta Sadik Hassan ya ce sun gudanar da ayyukansu cikin nasara kasancewa a duk aikin da suka yi babu wanda ya zo da wata matsala.

Dokta Sadik ya bayyana bukatar da ke akwai ga jama’a musamamn wadanda suka kai shekara 40 su rika ziyaratar asibiti don duba lafiyar idanunsu a duk bayan wata shida.

Mafi yawan wadanda suka amfana da shirin sun bayyana gadiyarsu ga dan majalisar sakamkon taimaka musu da ya yi inda suka samu lafiyar idanunsu bayan daukar tsawon lokaci ba su gani da su

Malam Dahiru Tela Yankatsari mai shekara 74 wanda a yanzu yake gani bayan aikin cire masa yana da aka yi a idanunsa na hagu ya ce ya shafe shekara 10 yana fama da cutar idanu. “Na je asibitoci da dama amma ban samu magani ba sai a yanzu. Ban taba zaton za a yi min aiki cikin kankanen lokaci in warke ba. A yanzu ina gani tar da idona na hagu. Ina godiya ga dan majalisa Allah Ya saka da alheri,” inji shi.

A karshen shirin ayarin likitocin ya yi wa marasa lafiya kimanin 500 aiki, yayin da ya raba gilasai na karin gani guda 500. Haka kuma an bayar da magani ga akalla mutum 1,800 a lokacin gudanar da shirin.