✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar gini a Delta

Ranar Asabar ta makon jiya ne wani gini mai hawa uku da ke Abraka, a Karamar Hukumar Ethiope ta Gabas da ke Jihar Delta, ya…

Ranar Asabar ta makon jiya ne wani gini mai hawa uku da ke Abraka, a Karamar Hukumar Ethiope ta Gabas da ke Jihar Delta, ya rufta inda ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu yayin da aka ceto wadansu da ginin ya raunata. Hadarin ya auku ne a Unguwar Aghawana. Aminiya ta gano cewa lokacin da ginin ya ruguje akwai leburorin da suke aiki a benen da ake zaton sun kai mutum 12.

Majiyarmu ta ce, mutum hudu da suka mutu suna barci ne a hawa na biyu na ginin lokacin da lamarin ya faru wanda ta haka ne ya yi sanadiyar ajalinsu.

Wani makwabcin ginin da ya rushe mai suna Mista Oghenebwegba, ya shaida wa manema labarai cewa, “Ina dora alhakin rushewar ginin kan sakaci, kamata ya yi a kama mai gidan domin an yi amfani da bulo-bulo marasa kwari da inganci a wajen aikin ginin.”

A ’yan kwanakin nan ana samun faduwar gini a sassa daban-daban na kasar nan, na baya-bayan nan shi ne wanda aka samu a Jos babban birnin Jihar Filato lamarin da ake danganta shi da yin amfani da kayan gini marasa inganci, ko dora ginin bene a kan ginin da tun farko ba shirya yin bene mai hawa sama da daya ba.