✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 sun mutu bayan kwalekwale ya kife da su a Nasarawa

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai a wani kwalekwale da ke tafiya a kogin Gwayaka a yankin Gabas na Karamar Hukumar Lafiya…

Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai a wani kwalekwale da ke tafiya a kogin Gwayaka a yankin Gabas na Karamar Hukumar Lafiya a jihar Nasarawa.

Wani ganau ya bayyanawa Aminiya cewa, wadanda suka rasa rayukan nasu manoman rani ne ‘yan jihar Kano, kwalekwale ya kife da su ne da yamma lokacin da suka dawo gona suna tafiya zuwa gida.

Rahotan ya kara da cewa, akwai yiwuwar cewa kwalekwale ya yi hadarin bayan ya dauko fasinjoji 20 wanda hakan yasa nauyi ya yi masa yawa.

A shekarar da ta gabata be ne aka samu rahoton kifewar kwalekwale a wannan Karamar Hukumar a Kogin Ashangwa.