✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 700 sun rasu sanadiyar Guguwar ‘Idai’

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce adadin mutanen da suka rasu a kasashen yankin Kudancin Afirka sanadiyar mummunar guguwar nan da aka wa lakabi da ‘Idai’…

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce adadin mutanen da suka rasu a kasashen yankin Kudancin Afirka sanadiyar mummunar guguwar nan da aka wa lakabi da ‘Idai’ ya haura mutum 700.

Sama da mutum 400 sun rasu ne a Mozambikue, inda masu ba da agajin gaggawa ke ta kokarin taimaka wa dubban mutane.

Ministan Filaye da Muhalli a Mozambikue, Mista Celso Correia, ya ce “Ana cikin wani mawuyacin hali, amma ana samun sauki.”

Ya kara da cewa akwai akalla mutum 1,500 da ke saman rufin gidaje da bishiyoyi, wadanda suke so a ceto su, sannan kusan mutum dubu 89 sun koma sansanin ’yan gudun hijira.

Baya ga kasar Mozambikue, akwai kasashen Zimbabwe da Malawi da su ma suke kokarin farfadowa daga wannan mummunar guguwa.

Masu ayyukan ba da agaji sun ce tabbas adadin mutanen da suka rasu a kasashen uku zai karu, yayin da ambaliyar ruwan ke janyewa.

Akalla mutum miliyan daya da dubu 700 guguwar ta shafa, wacce ba a taba ganin guguwa mai karfinta a yankin ba cikin shekaru masu yawa da suka gabata.

Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Mark Lowcock, ya ce, majalisar ta saka kokon neman taimakon Dala miliyan 282, don a tallafa wa wadanda bala’in ya shafa.

Ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen samar da ruwan sha da magunguna da tsabtace muhalli da samar da abinci da kuma taimaka wa al’umar da bala’in ya shafa domin su koma bakin sana’o’insu.

Kungiyar Agaji ta Red Cross da Red Crescent, sun nemi taimakaon Dala miliyan 30 da rabi, domin a samar da kayayyakin agaji ga mutum dubu 200 da suka fi galabaita sanadiyar guguwar kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

Sakatare Janar na kungiyoyin, Elhadi As Sy, ya nuna bukatar samar da wadannan kudade, bayan wata ziyarar da ya kai wani sansanin da mutane suka fake, inda ya ce, “Daya daga cikin inda na ziyarta makaranta ce, tana dauke da mutum dubu uku, kuma ajujuwa 15 ne kacal a makarantar, ban-daki shida, sannan ita kanta makarantar, ambaliyar ruwa ta mamaye wani sashinta.”