✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Morsi ta bar baya da kura

Majalisar dinkin duniya ta yi kiran da a gudanar da bincike mai zaman kansa game da mutuwar bagtatan da tsohon shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi…

Majalisar dinkin duniya ta yi kiran da a gudanar da bincike mai zaman kansa game da mutuwar bagtatan da tsohon shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi yayi.

Ofishin Kare Hakkin dan Adam na majalisar, ya ce akwai damuwa kan yanayin da Morsin ya samu kansa a gidan kaso, da suka hadar da yadda baya samun cikakken duba lafiyarsa tare da share lokaci mai tsawo yana tsare shi kadai a dakin kurkuku.

Su ma kungiyoyin kare hakkin bil’adama, wadanda suka yi Allah-wadai da halin da aka tsare shi a ciki, sun yi kiran da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan musabbabin mutuwarsa.

Tsohon shugaban mai shekara 67 ya yanke jiki ya fadi lokacin sauraron bahasinsa kan zarge-zargen leken asiri a kotun birnin Alkahira.

Sai dai an rufe shi ne da jijjifin safiyar Talata, a gaban iyalansa.

Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi da ya kasance membanta, ta zargi mahukuntan birnin Alkahira da laifin yiwa Morsin kisan mummuke kuma da gangan, a shekaru shidan da ya shafe a kurkuku.

Sai dai kasar Masar din da kakkausar lafazi ta yi tir da kiran nan majalisar dinkin duniyar, tana mai alakanta kiran gudanar da bincike mai zaman kansa game da mutuwar Morsin, a zaman yunkurin saka siyasa a kan batun.

Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ruwaito kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar, Ahmed Hafez yana cewa, da babbar murya Masar ta yi Allah wadai da kiran na majalisar dinkin duniyar, ta kuma kafe kai da fata cewa ‘mutuwar Morsi, ta Allah da Annabinsa ne.’

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana Mursi a matsayin shahidi.

“Ganin yadda marigayin, wadda aka yi wa shari’ah a kotun juyin mulki kuma aka yanke masa hukuncin kisa, ya ja numfashinsa na karshe a kotu, hakan wata manuniya ce ta gallazawar da aka yi masa tsawon shekaru, shi da jama’arsa.

Istanbul na Turkiyya sun yi masa sallar janaza

Erdogan ya ce zai rike shugabancin kasar Masar na Abdel Fateh al-Sisi da alhaki kuma tarihi ba zai taba mantawa da ’yan kama-karyan da suka yi sanadin mutuwar Morsi ba.

Shi ma wani dan majalisar dokokin Burtaniya na jam’iyyar Conserbatibe, Crispin Blunt, wanda ke daya daga cikin mutanen da suka yi ta bayyana damuwa bara game da yadda ake tsare da shugaban, ya bukaci gudanar da bincike na kasashen duniya.

Ya fada wa BBC cewa halin da aka tsare Morsi ya yi muni matuka, kuma sun fada a lokacin, cewa idan ba a kula da lafiyarsa cikin gaggawa ba, hakan zai yi lahanin dindindin ga lafiyarsa, ko ma ya zama sanadin cikawarsa.

“Kuma ga shi yanzu abin da muka fada ya tabbata, don haka sai a gudanar da bincike mai zaman kansa, don tantance musabbabin rasuwarsa,” in ji Crispin.

Daya daga cikin masu adawa da Morsi, Khaled Dawoud na jam’iyyar National Salbation Front, ya ce ba a yi wa marigayin adalci ba.

A cewarsa su jam’iyya ce da ta rika kiran a mutunta doka, a mutunta hakkin dan Adam kuma ya ce ya yi imani an hanawa Morsi wasu daga cikin hakkokinsa na bil’adama ciki har da ’yancinsa na samun kula da lafiya.

Ma’aikatar cikin gidan Masar dai ta sanya kasar cikin ta-kwana.

Rasuwar Mohammed Morsi ta zo ne ’yan kwanaki gabanin fara gasar cin kofin Afirka da Masar ke karbar bakunci.

Iyalansa da kuma masu fafutuka sun dade suna kokawa kan tabarbarewar rashin lafiyarsa da kuma lokutan da ake tsare shi shi kadai bayan ’yar ganawar da yake yi da lauyoyinsa da kuma iyalansa.

Dansa, Abdullah Mohammed Morsi, ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mahukuntan Masar sun ki amincewa da bukatar iyalansa na a basu gawarsa domin yi masa jana’iza a bainar jama’a a mahaifarsa.

Wane ne Morsi?

An haifi Morsi ne a kauyen El-Adwah a gabar kogin Nilu a lardin Sharkiya a 1951.

Ya yi karatu a fannin injiniya a Jami’ar birnin Alkahira a shekarun 1970 kafin ya tafi kasar Amurka inda ya kammala digiri na uku a can.

Shi ne zababben shugaban kasar Masar na farko, wanda sojoji suka hambarar bayan shekara daya kawai a kan mulkin a ranar 3 ga watan Yulin 2013.

A matsayin dan majalisa, an sha yabonsa kan yadda yake da fasahar iya zance, kamar yadda ya yi a 2002 lokacin da aka samu hatsarin jirgin kasa, inda ya soki gazawar gwamnati.

Karan Morsi ya kai tsaiko a kungiyar ’Yan’uwa Musulmi bayan ya zama dan majalisar kasa a matsayin Indifenda daga shekara ta 2000 zuwa 2005.

Kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Brotherhood ta tsayar da shi dan takarar shugabancin kasar Masar a shekarar 2012.

Bayan da ya samu nasara a zaben 2012, ya yi alkawarin cewa “gwamnatinsa za ta tafi da dukkan ’yan Masar.”

An zarge shi da barin masu tsananin kishin addinin Islama cin karensu ba babbaka a fagen siyasar kasar da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar, batun da shi da magoya bayansa suka musanta.

Daga nan ne aka fara samun dimbin masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Morsi a titunan kasar lokacin bikin cika shekara daya da hawansa mulki a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2013.

Sojoji sun gargadi Morsi cewa za su shiga cikin rikicin matukar bai gamsar da ’yan kasa ba, kuma suka ba shi kwana biyu a matsayin wa’adi.

A yammacin 3 ga watan Yulin 2013, sojoji suka dakatar da kundin tsarin mulkin kasar sannan suka sanar da kafa wata kwarya-kwaryar gwamnatin kwararru ta wucin-gadi kafin sabon zabe.

Morsi ya yi Allah-wadai da wannan yunkuri a matsayin juyin mulki

Bayan haka sai sojojin suka kama Morsi, wanda ya yi watsi da matakin hambarar da gwamnatinsa.

Wata hudu bayan hambarar da shi aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da sauran mutum 14 na kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood, inda aka zarge su da iza magoya bayansu wajen kisan masu zanga-zanga.

A zaman kotun na farko, Morsi ya daga murya daga cikin kejin da ake tsare da shi a cikin kotu yana mai cewa: “Ni aka zalunta da juyin mulki” sannan kuma ya yi watsi da ikon kotun na shari’ar da take yi masa.

Daga baya kuma aka yanke masa hukuncin kisa bayan tuhumarsa da wasu karin laifukan, kafin daga bisani a janye hukuncin.

An wanke shi daga zargin kisan kai amma an daure shi shekara 20 bisa umarnin da ya bayar wajen tsarewa da kuma azabtar da masu zanga-zanga.

Ya rasu ne yayin da ake tsaka da yi masa shari’a a harabar kotu ranar 17 ga watan Yunin 2019.