✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na fara kidan gurmi don na raya al’ada – danzuru Maigurmi

Wani matashi mai suna Aliyu danzuru Maigurmi dan shekara 28 a duniya da ke kidan gurmi da waka ya ce ya shiga sana’ar kidan gurmi…

Wani matashi mai suna Aliyu danzuru Maigurmi dan shekara 28 a duniya da ke kidan gurmi da waka ya ce ya shiga sana’ar kidan gurmi ne don ya raya al’ada, wanda ya ce a yanzu kade-kade na zamani suna neman mayar da na da tarihi.
Aliyu danzuru dan asalin Jihar Kebbi ne da ke zaune a Jihar Legas ya bayyana hakan ne a lokacin da ya tattauna Aminiya a makon jiya.
danzuru ya ce: “Tun ina makarantar firamare nake jin ana yin kidan gurmi a rediyo sai kawai na ji ina sha’awa. Daga nan sai na fara yi kadan-kadan. Da na kammala makarantar firamare sai ya zamana na kware wajen yadda ake kidan gurmi. Da na dan kara girma na ga na yi wayo sai na yanke shawarar na shigo bariki na nemi abinci. Sai Allah ya hada ni da iyayen gida na kirki wadanda suka rika taimaka mini ina samun na abinci.”
Ya ci gaba da cewa, “Dalilin da ya sa na shiga wannan sana’a shi ne, na ga yadda kade-kade na da suke neman zama tarihi, shi ya sa na yi alwashin ba da gudunmuwata wurin raya kidan gurmi. A yanzu nakan yi sutura da ciyar da iyalina da iyayena.”
Ya bayyana cewa sana’ar kidan gurmi na bukatar hakuri da juriya sannan kuma tana bukatar  yin biyayya ga manya.
Ya dage a kan cewa hakurin da ya yi shi ya kai yanzu har gida jama’a ke bin sa domin su gayyace shi wasa.
To amma Aliyu ya bayyana cewa babban abin da yake damun sa shi ne irin yadda wasu ke yi wa masu kidan gurmi kallon raini.
‘Mu ba sata muke yi ba, sana’a ce wacce Allah Ya hukunta sai mun ci abinci a cikinta, amma sai ka ga wasu na yi mana kallon banza duk da haka mun gode wa Allah, wasu na girmama mu kuma suna ba mu kudi idan muka hadu da su.” Inji shi.