✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gina gida da sana’ar kafinta – Binta Kafinta

Malama Binta Muhamamd wacce aka fi sani da Binta Maicarbi kafinta ce da ke gudanar da sana’ar kafinta a unguwar Kabuga cikin Jihar Kano. A…

Malama Binta Muhamamd wacce aka fi sani da Binta Maicarbi kafinta ce da ke gudanar da sana’ar kafinta a unguwar Kabuga cikin Jihar Kano. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana cewa ta fara sana’arta ne da Naira dubu daya wacce a yanzu ta kai ga gina gidan kanta da ribar da take samu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Me ya ja ra’ayinki kika shiga sana’ar kafinta duba da cewa ana ganin sana’a ce da maza?

Zan iya cewa sha’awa ce kawai da kuma rabo. Da na fara kuma sai na ji ina son abin don haka na kara jajircewa don na nuna wa duniya cewa  mata ma jarumai ne wajen neman na kansu. Duk da cewa ba komai ne mace za ta iya yi ba, amma akwai abubuwa da dama da mata za mu yi kamar maza. Ga shi yanzu na dauki kimanin shekara 17 ina wannan sana’a.  Ina yin aikin gado da kujeru da sauransu. Babu abin da ba na yi na aikin sarrafa katako tun daga kan fila da feshi da sanya yadin kujeru. Nakan je titin France rod na sayo katakona da sauran kayan aikin sai na zo

na yi aikin  goge shi. Daga nan sai na yanka na fitar da kowane abu da nake son kerawa sawa’un gado ne ko kuma kujeru. Idan na gama sai na zo na sa pila in goge. Sannan idan suka bushe sai in kunna inji na goge su wato na yi musu feshin fenti.  Duk da cewa mun fi yin sababbin kaya, amma muna sayen tsofaffin kaya don sayarwa kodayake a lokuta da dama sai na sake gyara su sannan nake sayar da su.

Shin kin fuskanci kyama daga wurin ‘yan uwanki mata ko kuma abokan sana’arki maza wadanda za su ga sana’arsu ce kika yi wa shisshigi?

A gaskiya da farko na fuskanci wannan matsala, amma a yanzu da rayuwa ta sauya kowa ya fito neman na kansa mun zama abin sha’awa a tsakanin ‘yan uwana mata, domin a yanzu da kansu suke zuwa sayen kayana, kuma su kawo min masu saye har ma na ba su wani abu. Haka kuma su kansu maza kafintocin sun nuna min kyama domin za ki ga yadda suke kushe wa mutum aiki a maimakon su karfafe shi. A wasu lokuta ma zan so shago na tarar an kone min kaya, amma da na yi hakuri ga shi komai ya wuce.

A matsayinki na mace yaya kike yi wajen hada aikin gida da kuma sana”arki?

A baya dai na sha wahala ta zirga-zirga, amma cikin ikon Allah da yake na kuduri aniyar cewa zan iya yi sannan kuma maigidana ya bani goyon baya, hakan na rika hada wadanan abubuwa biyu. Cikin ikon Allah ga shi har yanzu muna ci gaba da yi. Yanzu kuwa abin ya yi sauki domin ina da budurwar yarinya a gida wacce take taimaka min da ayyukan gida. Yawanci ina zuwa shago da misalin karfe 11 na safe sannan aduk lokacin da karfe hudu ta yi to na koma gida. Sai dai idan da wani abu muhimmi da zai tsayar da ni.

Wacce nasara kike jin kin samu daga wannan sana’a?

Babu shakka ina takama da wannan sana’a tawa, domin da ita nake rike da iyayena da ‘yan uwana. Baya ga filaye da na mallaka da wannan sana’a na gina gida. Haka kuma na mallaki shaguna da nake zuba kayana a ciki. Alhamdulillahi babu abin da zan ce sai godiya. Idan an duba na fara wannan sana’a ne da Naira dubu daya kacal. A wancan lokaci nakan je na  sayi ‘yan kayan katako na hannu na kai wa masu saye su saya. Yau da gobe ina yin haka har na sami jari na fara wannan sana’a.

Wane irin matsaloli kike fuskanta a wannan sana’ar?

A gaskiya akwai kalubale musamman wasu lokutan mutane za su sanya a yi musu aiki a dauka akai musu wasu garuruwa kamar Zariya da Zamfara da Fatuskum, bayan mutum ya sa kudinsa ya yi aikin ga kuma kudin motar daukar kaya da ya biya, idan aka kai musu kayan sai su ki biyan kudin.  A wasu lokutan kuma mutane suna sanya wa a yi musu aiki sai kuma su kasa biyan cikon kudin kayan, haka za a bar mutum da kaya sai dai ya saka a kasuwa.

Mmutane nawa ne ke karkashinki?

Kin san da yake mutanen suna zuwa suna tafiya ne. idan mutum ya dade a hannuna ya koyi aiki nakan yaye shi shi ma ya je ya kafa nasa shagon don cin gashin kansa.  A yanzu haka irin wadanan mutane suna nan suna gudanar da sana’arsu ta kafinta a wurare daban-daban. A halin yanzu dai akwai mutane takwas da ke zuwa su yi aiki a karkashina wadanda kuma suke samin na abinci a kullum.

A lokuta da dama ana kuka da ku kafintoci game da rashin cika alkawari me za k ice akan hakan?

Gaskiya ne wannan, wanda kuma a tunanina hadama ce take kawo hakan. Ban sani ba ko don kasancewata mace ba na hada wa kaina aiki da yawa, ma’ana idan na ga aiki ya yi min yawa idan an kawo min aiki nakan gaya wa mutam halin da ake ciki, inda nake kai su wasu wuraren.

Wace shawara za ki ba ‘yan uwanki kafintoci a kan hakan?

Ina shawartarsu da su rike gaskiya da amana, domin duk abin da mutum zai yi idan babu wadannan abubuwa  to ba zai sami nasara ba. A mastayinka na kafinta idan har mutum ya nemi ka yi masa aiki har ya dauki kudinsa ya ba ka kuka tsayar da lokaci to kamata ya yi ka yi kokari ka yi masa. A gaskiya Allah Ya yi wa wannan sana’a tamu albarka, akwai rufin asiri a cikinta.

Wane kira kike da shi ga gwamnati ta yadda za a inganta muku wannan sana’a taku?

Ina ganin ya kamata gwamnati ta dube mu musamamn matan da ke cikin wannan sana’a ta yi kokarin bunkasa mana wannan sana’a tamu ta hanyar ba mu jari sosai yadda za mu rika gudanar da wannan sana’a. A wasu lokutan kin san yadd mata suke babu karfin jari, sai ki ga abubuwan ba sa yin daidai. Muna bukatar gwamnati ta kawo mana dauki. Muna bukatar kayan aiki na zamani saboda har yanzu da tsofaffin kayayyaki muke amfani. Muna so kuma gwamnati ta ba mu fili da za mu rika zuba kayanmu idan mun kera. Zan kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan uwana mata da mu tashi mu nemi na kanmu kasancewar zamnani ya canza dole sai mace tana neman na kanta sanann abubuwan gida suke tafiya daidai. Ba duk namiji ne zai iya biya wa mace bukatunta ba. Ina kishin na ga ‘ya mace tana kwance babu sana’a. don haka akwai bukatar mata su tashi su jajirce domin su dogara da kansu.