✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na gwammace in koma Jubentus maimakon Real Madrid – Pogba

Dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United da ke Ingila kuma dan asalin Faransa Paul Pogba ya bayyana cewa ya gwammace ya koma kulob…

Dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United da ke Ingila kuma dan asalin Faransa Paul Pogba ya bayyana cewa ya gwammace ya koma kulob dinsa na da wato Jubentus da ke Italiya maimakon ya koma Real Madrid da ke Sifen a kaka mai zuwa.

Kulob din Jubentus da na Real Madrid suna rububi a kan dan kwallon ne da aka kiyasta kudinsa a kan Fam miliyan 150 (kimanin Naira biliyan 70 da miliyan 650 )kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta Sky Sport ta ruwaito.

Kimanin shekara uku ke nan da Pogba ya canja sheka daga Jubentus zuwa na Manchester United a kan Yuro miliyan 100.

A makon jiya ne dan kwallon ya sanar da mahukuntan United cewa yana son ya canja sheka zuwa wani kulob kafin a fara kaka mai zuwa.

Yanzu dai masu bibiyar wasan kwallon kafa sun zuba ido su ga kulob din da Pogba zai koma.

Pogba yana daga cikin ’yan kwallon da suka lashe wa Faransa Kofin Kwallon Kafa na duniya a bara.