Da Dumi Dumi

Na sa kyautar mota a gasa kan wakar Hanta da Jini – Nazifi Sharif

Nazifi Sharif wani fitatcen mawakin siyasa ne da ke zaune a Kano,  ya ce ya sanya gasa kan wakar da ya yi wa Sanata Uba Sani na Kaduna ta Tsakiya, mai suna Hanta da Jini, inda ya yi alkawarin bayar da kyautar sabuwar mota, ga duk wanda ya zo na daya a  gasar. A tattaunawa da wakilinmu, ya bayyana yadda aka yi ya shiga waka da nasarorin da ya samu da abin da ya karfafa masa gwiwar sanya wannan gasa:

 

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihin rayuwarka?

Nazifi Sharif: An haife ni ne a Unguwar Indabawa a Kano. Kuma na yi makarantar boko da ta  allo da ta islamiyya. Na fara makarantar boko a firamaren  Dan Agundi, kuma na yi karamar sakandare a Sabuwar Kofa. Kuma na yi babbar sakandare a Sakandare ta Sharada. Daga nan na tafi Makarantar Koyon Shari’a ta Kano, amma ban kammala ba, na tafi kasar Saudiyya.

Bayan da na dawo daga Saudiyya, sai na kama sana’ar rini. Daga nan na koma harkokin kasuwanci a Kasuwar Kantin Kwari, har yanzu ina da shago a kasuwar.

ADVERTISEMENT

Bayan haka ina harkokin sayar da motoci, kuma ina da asibiti mai zaman kansa mai suna Sharif Hospital a nan Kano.

Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar shiga harkokin waka kuma a wane lokaci ne ka fara wakar? 

Nazifi Sharif: Na fara waka ce tun a shekarar 2003. Kuma na shiga harkar waka ce bisa dalilin son da nake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau lokacin da yake Gwamnan Jihar Kano. Saboda wakokin da na ji ana yi masa a lokacin, shi ne na ce ni ma bari in koma waka, domin in yi masa waka. Shi ne na rubuta masa wata waka, mai suna Allah Maimaita, kuma na rerata a lokacin.

Aminiya: Daga lokacin da ka fara waka zuwa yanzu ka yi wakoki kamar nawa?

Nazifi Sharif: Gaskiya ba zan iya fadin yawan wakokin da na yi ba, saboda mafiya yawan wakokina na siyasa ne. Domin idan muka hadu da dan siyasa, mukan yi masa wakoki daban-daban, tun daga fitowa takara da zuwa yakin neman zabe, har a kai ga zaben. Kuma kamar a Jihar Kano da ake yin abubuwa na siyasa, da zarar an yi wani abu na siyasa ya taso za mu yi waka.  Kuma na yi wa ’yan siyasa daban-daban wakoki, don haka zai yi wuya na iya sanin adadin wakokin da na yi. Kuma wakokin siyasar da nake yi, na fi mayar da hankali a bangaren jihohin Kano da Bauchi da Adamawa.

Aminiya: Zuwa yanzu wadanne nasarori ne kake ganin ka samu a waka?

Nazifi Sharif: Gaskiya na samu nasarori da dama a waka, domin wakar da na fara yi a Kano ta Alhaji Sani Lawal Kofar Mata wani na kusa da Malam Ibrahim Shekarau a lokacin da yake Gwamna, mai suna Mu Gaishe Da Barde a lokacin da na yi wakar, an ba ni kujerun aikin Hajji har guda uku.

Bayan haka na yi gida, na yi aure na yi motoci na hawa sama da 26 duk da waka. Don haka babu abin da zan ce wa harkar waka, sai dai in yi wa Allah godiya.

Aminiya: A duk wakokin da ka yi, wacce ka fi so?

Nazifi Sharif: Tunda na fara waka ban samu wakokin da suka kwanta mini a rai ba, kamar wakokin nan guda biyu, da na yi wa Sanata Uba Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya mai suna Hanta da Jini da kuma wakar Sabuwar Kaduna ta Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El’rufa’i. Wannan waka  mai suna Sabuwar Kaduna ba ta fito ba. Amma na riga na kammala daukarta a murya da bidiyo.

Wannan waka da na yi wa Sanata Uba Sani, na yi ta ce bisa wasu dalilai, kuma na samu wannan waka kamar yadda nake so, kuma shi ma wanda na yi wa wakar yana kasar waje ya kira ni ya ce wakar ta yi masa, ya ji dadi sosai.

Saboda yadda ya nuna mini ya ji dadin wakar, ya sa na sanya gasa a kan  wakar. Wanda ya ci na daya zan ba shi mota sabuwa wanda ya ci na biyu zan ba shi kyautar Keke NAPEP sabo, wanda ya ci na uku zan ba shi kyautar babur sabo. Daga nan wadanda suka ci har zuwa na goma, zan ba su kyautar Naira dubu 50, kowannesu.

An fara wannan gasa ce a wannan wata da muke ciki, kuma za a rufe a ranar 30 ga wannan wata da muke ciki. Kuma tsarin da muka bi wajen shirya gasar, mun yi talla a kafofin sada zumunta na Intanet. Kuma gasar ana gudanar da ita ce ta kafofin sada zumuntar. Mutum zai yi kwalliya mai kyau, kuma ya iya bin wannan waka kamar yadda aka yi ta, ya yi rawa ya dauki hoton bidiyo ya tura ta Instagram.

Za mu yi gagarumin taron raba kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara a gasar a ranar Lahadi 12 ga Afrilu a garin Kaduna. Zuwa yanzu sama da mutum 500, maza da mata sun shiga gasar.

Shi ma da kansa Mai girma Sanata Uba Sani ya ce a wannan taro zai zo ya bayar da gudunmawa, ta hanyar tallafa wa nakasassu da kekunan guragu da abubuwan hawa ga masu karamin karfi.

Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga mawaka ’yan uwanka?

Nazifi Sharif: Kirana ga mawaka ’yan uwana shi ne mu rika mutunta wannan sana’a. Kuma mu rika kyautata wa jama’a, kuma mu rika tallafa wa na kasa da mu a wannan sana’a sannan mu rika janyo su a jika muna tallafa musu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya