Search
Subscribe
Na sha zagi kan mayar da Naira miliyan 15 da na  tsinta – Kofur Umar

Babban Hafsan Sojan Sama, Iya Mashal Sidique Abubakar yana daura wa Umar igiyar muqaminsa, a wani qwarya-qwaryan biki da aka gudanar a Abuja, a tsakiya mahaifinsa ne yake kallo.

Na sha zagi kan mayar da Naira miliyan 15 da na  tsinta – Kofur Umar

Kofur Bashir Umar sojan saman Najeriya ne da a makon jiya ya tsinci Yuro dubu 37 (kimanin Naira miliyan 15) da wani ya yar a filin Jiragen Saman Aminu Kano amma ya mayar wa mai kudin da abinsa. Kafin faruwar wannan lamari, Bashir kurtu ne, amma sanadiyyar wannan abin kirki da ya yi aka kara masa girma har rubi biyu, daga kurtu zuwa Kofur. Baya ga wannan karin girma, Babban Hafsan Sojan Sama, Iya Mashal Sidikue Abubakar da kansa ya daura masa igiyar mukaminsa, a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar. Aminiya ta gana da sojan saman mai gaskiya, inda ya bayyana yadda al’amarin ya faru da kuma abin da ya biyo baya:

Ko za ka bayyana mana abin da ya faru a ranar da ka tsinci wannan kudi?

Mun dawo daga sintiri ne da maraice sai na ga ambulan a gefen hanya. Ina tare da sauran abokan aikina, sai na duka na dauka, amma ban bari abokan aikina sun san abin da ke cikin ambulan din ba. Na samu lambar tarho rubuce a jikin ambulan din, don haka lokacin da na isa cikin bariki, sai na kira lambar wayar nan. Bayan na kira sai na ji wani mutum ya amsa. Na shaida masa cewa na tsinci wani kunshi. Sai ya ce mini ‘eh, wata ambulan mai ruwan kasa, mai dauke da sunan Alhaji Ahmed rubuce a jikinta ko.’ Daga nan sai ya ce mini wannan ambulan tasa ce, don haka mu hadu a wannan maraice. Na ce masa babu damuwa, ya zo Barikin Sojan Sama ya amshi kudinsa.

Mutumin kuwa ya zo, ya ajiye motarsa a waje, inda ni kuma na je na same shi. Na mika masa wannan kunshi da na tsinta, ya ce mini kudi ne a ciki, Yuro dubu 37 (kimanin Naira miliyan 15), nan take ya kirga kuma ya same su daidai. Ya yi ta yi mini godiya, sannan ya tambaye ni me zai ba ni a matsayin godiya kuma ya ce na taimake shi sosai, domin ba kowa ne zai tsinci kudin nan ya maida wa mai su ba. Na gaya masa cewa ba na bukatar komai domin kuwa ina samun bukatuna daga aikina. Na ce masa ya zubar da kudinsa, na gani kuma na maida masa, wannan shi ne kawai. Kan haka ya yi mini godiya ya yi tafiyarsa.

Bayan wani lokaci  muna hirar al’amarin da abokin aikina, wanda tare muka yi kwas din aiki da shi kuma a daki daya muke, mai suna Abubakar ashe ya ji ni lokacin da nake magana a waya da mai kudin, inda ya ji ina cewa ga inda zai zo ya same ni domin ya amshi kudinsa. Shi Abubakar din ne ya fara gaya wa mutane labarin abin da ya faru kuma daga nan ne  mutane suka san yadda al’amarin ya faru.

Lokacin da ka tsinci kudin ko ka yi kokwanto a zuciyarka, cewa ka rike su, kada ka nemi mai su ka mayar masa?

Daidai da sakan daya ban taba riyawa a zuciyata cewa in rike kudin ba, domin kuwa mahaifina a koyaushe yana koya mini cewa kada in taba kayan wani. Haka kuma yana gargadina cewa kada in sake in saka kaina cikin shaye-shayen kwaya da neman matan banza. Wannan shi ne dalilin da ya sanya tunanina ya ginu kan cewa ba zan taba kayan wani ba, kuma shi ya sanya nake cika alkawarin da na daukar wa mahaifina, cewa ba zan yi wadannan munanan halaye ba.

Tun daga lokacin da ka mayar da kudin ga mai su, wadanne irin maganganu ka rika samu daga ’yan uwa da abokan arziki?

Na sha zagi daga wadansu mutane, domin kuwa wadansu har ce mini suka yi ni matsiyaci ne, har abada ba zan yi arziki ba a rayuwata. Amma wadansu kuma sun yaba mini, don haka na samu maganganu iri daban-daban daga mutane dangane da wannan al’amari. Sai dai kuma ba na nadamar wannan mataki da na dauka, maimakon nadama ma, farin ciki na samu a lokacin da na mayar da kudin ga mai su.

Lokacin da ka yi ta samun yabo daga wurare daban-daban har a Shoshiyal Mediya, yaya ka ji?

Na ji dadi sosai, na yi murna, domin kuwa wadanda suka rika zagina za su gane wautarsu da yin haka. Don haka ina godiya ga wadanda suka rika nuna gamsuwa ga matakin da na dauka, kuma suka yaba mini.

Wace shawara za ka ba ’yan Najeriya, musamman wadanda suka samu kansu a irin yanayinka, suka tsinci dukiya a hanya?

Ina ba su shawara  cewa,  duk lokacin da mutum ya tsinci kayan wani, to ya yi kokarin mayar da shi ga mai shi. Mutum ya sani cewa koda daidai da Naira biyar ka dauka daga kayan wani, akwai hukunci na nan yana jiranka a Ranar Lahira. Kuma lallai sai ka biya mai hakki hakkinsa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin