✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na shiga takara ce don bai wa matasa kwarin gwiwa– Adnan Tudun-Wada

Kwamared Adnan Mukhtar Tudun-Wada matashin dan siyasa ne, marubuci kuma dan jarida da ke cikin matasan da suka shige gaba wajen fafutukar tabbatar da dokar…

Kwamared Adnan Mukhtar Tudun-Wada matashin dan siyasa ne, marubuci kuma dan jarida da ke cikin matasan da suka shige gaba wajen fafutukar tabbatar da dokar ba matasa dama a siyasa da shugabanci. Shi ne dan takarar Jam’iyyar UPC a mazabar Nasarawa a Majalisar Dokokin Jihar Kano. Aminiya ta tattauna da shi inda ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen kwato wa matasa da al’ummarsa ’yanci:

 

Mene ne tarihinka a takaice?

Sunana Adnan Mukhtar Tudun-Wada, an haife ni a garin TuduWada a Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano a 1992, mahaifina Barista Mukhtari Adamu Tanko lauya ne, mahaifiyata Malama Aminatu Usman Tudun-Wada malamar makaranta ce. Na yi firamare a Makarantar Maryam Memorial School, a 2004 na shiga Ahmadiyya College inda na yi karatun sakandare na kammala a shekarar 2010.

Tun ina sakandare na zama Shugaban Dalibai Musulmi da kuma magatakardan Kungiyar Dalibai masu rubuta labarai (Press Club) inda nake karanta labarai kullum a gaban taron dalibai.

A shekarar 2011 na shiga Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a  (CAS) da ke Kano inda na samu shiga Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke kano a shekarar 2014 na yi nazarin Addinin Musulunci fito babbar shaida ta Second Class Upper.

A jami’a na yi Mataimakin Kakakin Majalisar Dalibai wanda daga nan aka zabe ni na zama Magatakardar Kungiyar Dalibai ta Jami’ar. Mukamin da mahaifina Marigayi Barista Mukhtari Adamu ya rike a 1980 a  Kungiyar Daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Na yi aikin jarida da Daily Nigerian, sannan na yi rubuce-rubuce a kan shugabanci nagari da al’amuran kasada aka buga jaridun kasar nan. Ni mai sharhi ne a kan al’amuran da suka shafi al’umma shi ya sa ake yi min lakabi da Kwamared.

Me ya ba ka kwarin gwiwar shiga takarar dan majalisa a matsayinka na matashi?

Na shiga takara ce domin in bai wa matasa kwarin gwiwa. A matsayina na dan gwagwarmaya kuma tsohon shugaban dalibai da nake sahun gaba wajen ganin an rage shekarun tsayawa takara. Shi ya sa na ga ya dace in shigo a dama da ni domin in karfafa wa matsa kima in kare hakkin matasa da al’ummar kasar nan. Ciwon matashi sai matashi, rayuwar matasa na cikin wani hali a wannan kasa saboda haka babu wanda zai magance matsalar matasa sai matashi. Kasancewata shugaban dalibai ya ba ni kwarin gwiwa kwarai da gaske wajen ganin na shiga an dama da ni a siyasa domin kwato wa matasa ’yancinsu a daina amfani da su wajen daba da shaye-shaye da suka tsinci kansu.

Matasa ne kashi 65 na jama’ar kasa, saboda haka suna da damar da za su tabbatar da shugabanci nagari a kasar nan. Ba za ka taba kawo canji ba ga al’umma idan ba ka da dama ta shugabanci, wannan ne ya sa na shigo domin in samu damar da zan kawo wa al’ummata ci gaba.

Kasancewar ka tsaya takarar a  Jam’iyya UPC, ba ka tunanin za ka hadu da kalubale daga jam’iyyun PDP da APC?

Kalubale akwai shi tunda an lalata al’umma da siyasar kudi suna sayar da ’yancinsu. Ya kamata a ajiye siyasar APC da PDP a gefe domin duk abu daya ne. Al’umma su zo su gwada mutane masu nagarta a kowace jam’iyya suke. Ina kokari matuka wajen wayar da kan mutane a kan jam’iyyata da manufofina kuma ina da yakinin za su karbe su kamar yadda nake ganin nasara tun a wannan lokaci.

Ka taba yin jam’iyyun PDP da APC, me ya sa ka bar su ka koma sabuwar jam’iyya?

Saboda rashin adalci daga jagororin jam’iyyun, kuma ana ganin  ni talaka ne. Jagororin PDP da na APC sun zama ’yan Jari-Hujja. Saboda haka na tafi inda za a yi mini adalci kuma insha Allahu sai Allah Ya kunyata duk wanda ba ya son ya ga an taimaki matasa da talakawan kasar nan. Jagororin PDP a wancan lokacin sun nuna wa Kwankwaso ba zan tankwaru ba, ba za a juya ni ba, shi ya sa ya kawo wanda zai iya tankwarawa.

Yaya batun kudi da fafutikar yakin zabe kasancewa yanzu siyasa sai da kudi?

’Yan uwa da abokan arziki suna ba mu gudunmawa daidai gwargwado. Da yake ni ba zan bai wa kowa sisi ba, ina tunanin ya kamata a ce muna da hankalin da ba za mu sayar da ’yancinmu ba, mu tsaya mu zabi abin da zai amfani ’ya’yanmu da jikokinmu. Kudin da nake kashewa su ne kudin tafiyar da al’amuran yau da kullum. Amma ba zan ba wa kowa kudi ba kuma idan na shiga majalisa ma haka. An tura ni in je in yi doka kuma zan yi, zan gudanar da aikina kamar yadda na alkawarta. Ba zan daure wa siyasar bada kudi gindi ba.

Wane sabon abu matasa za su yi tsammani a wajenka?

Zan kawo kudirorin da za su inganta musu rayuwarsu, ba da jari domin su yi sana’a da kuma koya musu sana’o’i da za su dogara da kansu.

Yaya kake ganin za ka bambanta da sauran ’yan takara da zai sa mutane su zabe ka?

Manufofina su ne suke bambanta ni da su. Salon yakin neman zabena shi ma wani mizani ne. Ba zan yi wa al’umma karya ba, zan fada musu abin da zai yiwu ne da abin da zan iya. Babu yaudara a tsarina.

Wane kira kake da shi ga masu zabe musamman matasa?

Su yi zabe a kan cancanta, kada su bari a yi amfani da su wajen kawo hargitsi a ranar zabe, kuma su guji siyasar kudi da siyasar daba.