✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi nadamar kawo Gwamna dankwambo – Goje …Allah ne Ya ba dankwambo mulki ba Goje ba – Yayari

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Muhammad danjuma Goje ya nemi gafarar al’ummar jihar kan kawo Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ya zama magajinsa a zaben shekarar…

Sanata Danjuma GojeTsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Muhammad danjuma Goje ya nemi gafarar al’ummar jihar kan kawo Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo ya zama magajinsa a zaben shekarar 2011, inda ya ce hakan babban kuskure ne.
Sanata Goje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban jama a kananan hukumomin Yamaltu Deba da Akko da ke jihar a ranar Asabar lokacin zaben shugabannin Jam’iyyar APC na kananan hukumomi. Ya ce Allah Ya yi amfani da shi wajen ba dankwambo mulki, amma a yanzu yana nadama goya masa baya, kuma ya nemi al’ummar jihar su hada kai domin fatattakar gwamnatinsa a zaben badi.
Sanata Goje ya ce ya rungumi Jam’iyyar APC ne domin kawo canji a Gombe da kuma Najeriya bakin daya, inda ya ce APC za ta girmama ra’ayi da bukatun jama’a kuma wadda ba za ta yi barnar kudin jama’a ba, kuma za ta ceto Jihar Gombe da Najeriya daga rashin iya shugabanci da bakin mulki, don haka ya bukaci jama’a su hada hannu domin kawo canji mai amfani.
Furucin na Sanata Goje bai yi wa mukaraban Gwamna dankwambo dadi ba, inda suka kira taron manema labarai a Gombe suna masu cewa Allah ne kadai ke ba mutum mulki a lokacin da Ya so.
Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati kuma tsohon kwamishina a zamani mulkin Goje, Alhaji Ahmed Yayari ya ce Allah ne, ba Goje ne ya dora dankwambo ya zama Gwamnan Gombe ba, balle ya ce zai sauke shi, kuma idan ya manta su ba su manta ba a shekarar 2011 surukinsa Ibrahim Dasuki Jalo, ya so ya gaji kujerarsa, amma jama’ar Gombe suka ki, sannan ya tsayar da shi takarar dan Majalisar Tarayya, nan ma Mailantarki na APC ya yi masa mummunan kaye.
Alhaji Yayari ya ce maganar Sanata Goje tana kunshe da kuskure da kuma rashin fahimta. Ya ce tun kafin shekarun mulkin Sanata Goje su kare al’ummar Jihar Gombe ke ta zuwa wurin dankwambo a Abuja suna matsa masa ya fito ya nemi mukamin Gwamnan jihar. Sai ya ce ya kamata Sanata Goje, ya gane cewa Allah ke ba da mulki ba shi ba, da yake zancen a 2015 zai kwace mulki a hannun dankwambo.