Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Nadin Atiku: Waziri ba sai dan gado ke yi ba – Lamido

Lamidon Adamawa, Mai martaba Barkinxo Aliyu Mustapha

Mai martaba Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammmadu Barkindo Aliyu Mustapha ya  ce gudunmawar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bai wa Jihar Adamawa da kasa baki daya ba za su misaltu ba.

Lamido Barkindo ya fadi haka ne lokacin da yake nada Atiku Abubakar a matsayin Wazirin Adamawa na Bakwai a ranar Lahadin da ta gabata a Yola. “Waziri ba gado ake yi ba, kowa zai iya zama Waziri. Ina kira ga sauran sarakunan wannan jiha da su bai wa sabon Wazirin dukan hadin kan da yake bukata domin samun nasara a wannan sabon matsayi nasa,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo kira ya yi ga Waziri Atiku ya mai da hankali wajen hada kan al’umma.

Wakilin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma Ministan Abuja, Alhaji Musa Bello ya yi wa sabon Waziri fatan alheri a matsayin sakon Shugaba Buhari.

ADVERTISEMENT

Cikin wadanda suka halarci biki akwai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai, Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo da kuma gwamnonin jihohin Gombe da Sakkwato da Bayelsa da Taraba da sauran manyan baki.