Nadin mukamai: Buhari na ganawa da Gwamnonin APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Gwamnonin jam’iyya mai mulki ta APC na ganawa a fadar gidan gwamnati a Abuja, ganawar ta samu halartar shugaba Buhari da sauran masu fada aji wanda aka fara da misalin karfe 11:37 na safe a yau.

Gwamnonin jihohin da suka halarci ganawar sun hada da: Gwamnan Yobe da Osun da Ekiti da Edo da Filato da Neja da Kogi da Borno da Nasarawa da kuma Gwamnan jihar Ogun. Mataimakiyar Gwamnan Kaduna da Mataimakin Gwamnan Katsina duk sun halarci ganawar.

Yau kwana 21 da rantsar da shugaba Buhari, ana saran zai yi sabbin nadenaden mukamai nan gaba kadan.

Cikakken rahon na nan tafe.

 

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya