✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAFDAC ta garkame kamfanonin kera magungunan jabu a Kano

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC), ta garkame wasu kamfanoni biyu na hada magungunan dabbobi na jabu a jihar…

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC), ta garkame wasu kamfanoni biyu na hada magungunan dabbobi na jabu a jihar Kano.

Babban Jami’in Gudanarwa na hukumar shiyyar Kano, Shaba Muhammad, shi ne ya bayyana hakan ne yayin wani simame da jami’an hukumar suka kai karamar hukumar Bichi a ranar Laraba.

Ya ce simamen ya biyo bayan hukumar ta gano cewa ana baza hajar magungunan dabbobin na jabu masu yawan gaske a kasuwar Sabon Gari da sauran manyan kasuwanni da ke Jihar.

Mista Muhammad ya ce hukumar ta shafe tsawon watanni shida tana bin diddigin gano masu sarrafa jabun magungunan inda a ranar Talata dubunsu ta cika bayan an gano kamfanin da magunguna na kimanin naira miliyan goma.

A rahoton da jaridar Daily Nigerian ta wallafa, mamallakan kamfanonin Jamilu Muhammad Sani ya shiga hannu, kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.