Da Dumi Dumi

Najeriya a shekara 59

Babban Birnin Tarayya, Abuja da sauran manyan biranen jihohin kasar nan 36 sun sha ado da tutoci masu launin Kore da Fari da Kore tare da sauran kyallaye da balan-balan domin bikin tuna ranar ’yancin kan da Najeriya ta samu daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya shekara 59 da suka wuce. Sai dai ga wadanda a wancan lokaci sun riga sun girma kuma suke siyasa tun 1960 suna ganin shekaru 59 tamkar kiftawa da bismillah. ’Yan Najeriya na da dalilin nuna murnar hakan; sakamakon yadda kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya. Cikin wadannan shekaru kimanin 60, kasashe da dama sun kasa jure ire-iren wahalhalun da Najeriya ta yi fama da su a cikin shekara 59 da suka gabata. Akalla cikin shekara bakwai kawai daga samun ’yancin, Najeriya ta tsunduma cikin kazamin Yakin Basasar da ya yi kusan daidaita ta, wanda ya haddasa hasarar rayuka kimanin miliyan daya. Yanayin ya kasance mai matukar wuya, amma cikin shekara uku yakin ya kawo karshe cikin farin ciki da taken nan na “Babu wanda ya yi nasara kuma babu wanda aka rinjaya.” Ko baya ga Yakin Basasar, Najeriya ta yi fama da wasu matsaloli na tashe-tashen hankali. Watakila mafi muni cikinsu, shi ne rikicin Boko Haram da aka shafe shekara 10 ana fama da shi, wanda ya salwantar da rayuka kimanin dubu 40, galibi a yankin Arewa maso Gabas. Sai kuma na baya-bayan nan, wato rikicin ’yan bindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yamma da sace mutane ana garkuwa da su da kashe-kashe marasa kan gado da kai farmaki a kauyuka tare da satar shanu. Wannan mummunan yanayin ya kara kazancewa tare da rufa bayan rikice-rikicen manoma da makiyaya, da shi ma ya salwantar da dubban rayukan jama’a. A daidai ganiyar wadannan rigingimun da suka sha wa kasar kai, Najeriya ta samu damar sake gudanar da bikin murnar ranar ’yancin kanta.

Samun ’yancin kan Najeriya a 1960 ya zo ne da zumudi da dimbin fata kan abubuwa daban-daban. Marigayi Alhaji Sa Abubakar Tafawa Balewa, wanda shi ne Firayi Ministan kasar nan na farko, ya yi wasu bayanai masu sosa rai matuka a jawabinsa na samun ’yancin kan, “A wannan rana….. shi ne ya fi muhimmanci gare mu, sakamakon yadda muka jima muna jiran zuwan ranar; a yayin da aka jefa mu cikin jirar dole muna ji muna gani wasu kasashen na yi mana fintikau; yayin da muka kusan cimma muradinmu….. Mu da aka zaba a matsayin wakilan jama’ar kasar nan……. ba mu da damar fifita muradunmu na kashin kai domin gidajenmu……’yancin gudanar da harkokin siyasa ba zai wadatar ba face an samu rufa bayan kwanciyar hankali da tattalin arziki abin dogaro; kuma haka ba za a iya cimma muradun ba idan babu ’yancin ra’ayin kai na gaskiya da sakin mara da mutum zai iya bayyana ra’ayinsa da samun abubuwan da mutum ke muradi ko sha’awa…… tawayar tattalin arziki kan sanya sabuwar kasar da ta samu ’yanci cikin kangin fuskantar dukkan wani matsi, a wasu kasashen kuma hakan na hana al’ummomin kasashen ’yancin zabar irin gwamnatocin da suke so.”

Kusan shekara 60 bayan Tafawa Balewa ya gabatar da wannan jawabi, za a iya cewa dukkan wata sadarar jawabin nasa na da nasaba kai-tsaye da irin yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu. Har yanzu kasar nan ta gagara samun ’yancin gudanar da tattalin arziki abin dogaro da zai tafi kafada-da- kafada da ’yancin gudanar da harkokin siyasa. Kasashe irin su Koriya ta Kudu da Malesiya da Indonesiya har ma da Pakistan wadanda ya kamata a ce su ne tsararmu tun daga tasowa lokacin samun ’yancin kan siyasa, tuni sun yi mana fintikau a fagen bunkasar tattalin arziki sakamakon kyakkyawan tsare-tsaren tattalin arzikinsu na dogon zango. Najeriya har yanzu tana matsayin kurar baya a matsayin kasa mai dogaro sosai da shigo da kayayyakin da take da bukata daga waje, yayin da su kuma wadancan kasashe suka bunkasa tattalin arzikinsu inda suka zama masu fitar da kayayyakin kasashen nasu zuwa wasu kasashe. Dalilan koma bayan tattalin arzikin namun abin kaico ne. Tafarkin Najeriya ta fuskar bunkasa masana’antu ya samu tasgaro sakamakon rashin dorarrun manufofi daga gwamnatoci daban-daban cikin shekaru.

Ba za a iya cewa wai fatar gyara al’amuran ta dusashe gaba daya ba, a’a har yanzu da akwai sauran damar da ta rage mana wajen tsara kyakkyawar makomar ga kasarmu. Kasa kamar China tana da dogon tarihin sukurkucewar tattalin arzikinta, sai dai ta iya farfadowa daga wannan kangin cikin shekara 30 zuwa 40 da suka gabata inda ta zama abar misali a duniya. Damar gyara al’amuran ci gaban kasar nan na hannun masu mulkin kasar. Duk yake har yanzu kasar tana hade a matsayin kasa guda, amma akwai wagegen gibin da ke nuna bambance bambancen kabilanci da na addini da bangaranci da kuma na siyasa. Muddin aka ci gaba da samun ire-iren wadannan bambance bambancen, to ko shakka babu kasar nan ba za ta taba kaiwa tudun-mun-tsira ba. Domin yi wa tufkar hanci, akwai matukar bukatar lallai a hada kan kasar bisa turbar ci gaban zamantakewa da na tattalin arziki abin dogaro. Najeriya na da bukatar hadin kai na gaskiya da gaskiya da zama sama da bukatu na kashin kai, a daidai lokacin da kasar za ta hau turbar kyakkyawan makoma.

Muna yi muku murna da bikin samun ’yancin kai.

ADVERTISEMENT
Share