✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ke da kashi 15 na miyagun kwayoyi a duniya – Marwa

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (PACEDA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ya ce kwamitin mai mambobi 27 zai…

Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Dakile Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (PACEDA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) ya ce kwamitin mai mambobi 27 zai gabatar da shirinsa ga al’umma don tabbatar da muradun Shugaban Kasa kan dakile safara da shan miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.

Janar Marwa ya ce, illar shan miyagun kwayoyi na ci gaba da karuwa kamar yadda rahoton Hukumar UNODC ya sanar, wanda hakan ya kai kashi 10 cikin 100 yayin da Najeriya ke da kashi 15 cikin 100. Ya ce a za a iya saurin magance shan miyagun kwayoyi lokaci kadan ba, sai an bi wasu matakai.

Shugaban Kwamitin ya bayyana haka ne alokacin da mambobin kwamitin suka ziyarci hedikwatar Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a shekaranjiya Laraba.

Ya ce, kwanaki ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin kuma kwamitin ya bambanta da na sauran gwamnatocin baya. Ya ce, kwamitin ba kawai zai tunkari masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ba ne, har da hanyoyin da ake samowa da inda ake rarraba su don dakile illar da ke tattare da shan miyagun kwayoyin.

“Shugaba Muhammadu Buhari a shirye yake ya magance matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar nan, muna shirin nemo hanyar magance yaduwar shan miyagun kwayoyi a yankunan da ba sa mu’amala da kwayoyin,” inji Marwa.

Shugaban ya ce, yanzu haka kwamitin na shirin kaddamar da shirin yaki da shan miyagun kwayoyi kamar shirin yaki da rashin da’a (WAI).

A cewarsa, kwamitin zai fara shirin ne daga matakin kasa za a sanya sarakuna da shugabannin addinai a cikin a duk fadin kasar nan.