Da Dumi Dumi

Najeriya ta cika shekara 100 da kafuwa

A shekaranjiya Laraba ce Najeriya ta cika shekara 100 cif a matsayin dunkulalliyar kasa, bayan da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka hada lardunan Kudanci da na Arewacin kasar a ranar 1 ga Janairun 1914, kuma aka ba kasar sunan Najeriya.
Gwamna Janar Sa Fredrick Lugard ne ya jagoranci hade lardunan biyu da kuma yankin Legas don zama Najeriya bayan ya ajiye mukaminsa na Gwamnan Hong Kong a 1912.
Bayan kafa Najeriya Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya sun ci gaba da mulkin kasar har zuwa 1960 lokacin da suka mika mulki ga ’yan kasa sakamakon matsin lamba daga ’yan gwagwarmayar kwatar ’yanci da suka fito daga sassan kasar nan, wadanda galibinsu malaman makaranta ne da ’yan jarida da lauyoyi.
Najeriya ta fuskanci Yakin Basasa na tsawon shekara uku bayan samun ’yanci kai a 1960, sakamakon yunkurin ballewa da yankin Kudu maso Gabashin kasar da ya ayyana kansa a matsayin Jamhuriyyar Biyafara ya yi a 1967.
Duk da hasashen da wasu suka sha yi nna cewa kasar za ta wargaje kafin wannan lokaci, har yanzu kasar tana nan a matsayin dunkulalliya, kodayake akwai wasu kalubale da dama da take fuskanta. Kuma duk da wadannan kalubale ’yan Najeriya sun rika nanata goyon bayansu na kasar ta ci gaba da kasancewa a dunkule.
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya fadi yayin ibada a cocin Apostolic Faith Church da ke Jabi, Abuja cewa hade Arewa da Kudu don zama Najeriya wani al’amari ne daga Allah, inda ya ce daukakar Najeriya yana ta’allake ne da bambance-bambancenta da albarkatunta da kuma yawan jama’arta.
Ya ce, “Turawan mulkin mallaka sun hade sassan Najeriya a 1914. Kuma a ranar 1 ga Janairu mai zuwa (shekaranjiya), Najeriya za ta cika shekara 100. Kuma na amince da matsayin limaminmu cewa ba haka kawai hadewar ta faru ba, kaddara ce ta Ubangiji. Da Ubangiji bai so ba, hakan ba zai faru ba a lokacin, Arewa da Kudu ba za su hade ba. Hadewar Arewa da Kudu ta jawo Najeriya ta zama babbar kasa. Na ce Najeriya babbar kasa ce, ba saboda man fetur ba. Domin muna da kasashen da suke hako fetur fiye da Najeriya amma babu wanda ke maganarsu.”

Share