✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta haramta shigo da fitar kaya a iyakokinta

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da haramta shigo da fitar da kaya a iyakokin kasar da ke kan tudu har zuwa lokacin da Najeriyar za…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da haramta shigo da fitar da kaya a iyakokin kasar da ke kan tudu har zuwa lokacin da Najeriyar za ta samu cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.

Majiyarmu ta gano cewa, an fara taron da sauran kasahen makwabtan ne tun a ranar 20 ga watan Agusta 2019 wanda ya hada Hukumar da ke yaki da fasa-kwauri (Kwastam) Hukumar shige da fice ta Najerya tare da hadin gwiwar rundunar sojoji da wasu hukumomin tsaro.

Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali mai ritaya, ne bayyanawa manema labarai hakan yau Litinin inda ya ce zurgazigar kayayyaki daban suke da na mutane a iyakokin kasar.