✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta kasafta Naira tiriliyan 9  a badi

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na bana da ya kai Naira tiriliyan 8. da biliyan 830 ga Majalisar…

A shekaranjiya Laraba ce Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na bana da ya kai Naira tiriliyan 8. da biliyan 830 ga Majalisar Dokoki ta Kasa, inda Ma’aikatar Cikin Gida ta fi samun kaso mai yawa da ya kai Naira biliyan 569 da miliyan 700. Sai Ma’aikatar Tsaro Naira biliyan 435 da miliyan 620. Sai Ma’aikatar Ilimi da aka ware wa biliyan 462 da miliyan 240, inda Ma’aikatar Lafiya ke rufa musu baya da Naira biliyan 315 da miliyan 620.

An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta sayar da gangar mai miliyan biyu da dubu 300 a kullum. Kuma an tsara kasafin ne bisa hasashen farashin danyen mai a kan Dala 60 a kowace ganga. Kuma kan farashin canji Naira 305 kan Dala daya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha tafi da ihu a majalisar, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudin. Yana mai cewa wannan shi ne jawabinsa na karshe na gabatar da kasafin kudi a Majalisar Dokoki ta Takwas.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan Shugaban ya ce an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo masa sowa da ihu daga bangaren ’yan adawa a zauren majalisar.

Amma sai ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta yi aiki da yawa duk da ba ta samu kudi da yawa ba, a fannin noma da ayyuka da lantarki da kuma raya al’umma. Kuma ya ce a kowace jiha akwai aikin hanyoyi da gwamnatinsa ke yi.

Kuma ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen taimaka wa jihohi da tallafi domin biyan albashi da kudaden ’yan fansho. Sai dai ya ce a kasafin kudin akwai Naira triliyan 2 da biliyan 140 da aka ware domin biyan bashi.

Kasafin na badi ya zarce na bara inda Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali ne wajen kammala ayyukan hanyoyi da wasu na ci gaba da aka fara.

Ya ce, “Hauhawar farashin kayayyaki ta ragu daga kashi 18.17 a Janairun 2017 zuwa kashi 11.28 a Nuwamban bana. Kudin ajiyarmu ya karu daga Dala biliyan 28.57 a Mayun 2015 zuwa Dala biliyan 42.92 a tsakiyar Disamban bana. Mun yi kokari wajen magance matsalar tsaro a Arewa maso Gabas da rikicin kabilanci a wasu wurare.

“Mun samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa. Mun hana shigo da shinkafa daga waje. Mun samu nasarori wajen ayyukan ci gaba Mun yi kokarin kammala ayyukan da muka samu maimakon kirkirar wasu sababbi. A 2018 an yi aikin hanyoyi kilomita 1,531, an yi wa wasu kwaskwarima kilomita 1,008 a sassan Najeriya.

Game da dogara da kudaden da kasar za ta samu daga albarkatun mai, sai ya ce, ya umarci Kamfanin NNPC ya dauki dukan matakan da suka dace domin tabbatar da cimma burin fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu 300 a kullum.