✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta lallasa Lesotho har gida

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Super Eagles ta lallasa takwararta ta kasar Lesotho da ci 4-2 a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Afirka…

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kasa Super Eagles ta lallasa takwararta ta kasar Lesotho da ci 4-2 a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin Afirka da za a yi a shekarar 2021. Dan wasan Lesotho Masoabi Nkoto ne ya fara zira kwallo a ragar Najeriya a minti na 11 da fara wasa.

Dan wasan Najeriya Aled Iwobi ya farke  a minti na 22, yayin da Samuel Chukwueze ya zira ta biyu a minti na 38. Sai kuma Bictor Osimhen, ya ci ta uku da ta hudu a minti na 75 da 85.

Amma ba a tashi ba sai da Chidozie Awaziem na Lesotho ya cilla wa Najeriya kwallo ta biyu a zare a minti na 90. Super Eagles ce kan gaba a rukunin da maki shida, yayin da Benin take biye da ita da maki uku, sai Lesotho da Sierra Leon masu maki daidaya.

Sashin Hausa ba BBC, ya ce sau uku ke nan Najeriya tana doke kasar a irin wannan wasa, bayan ta casa ta a shekarar 2006 da ci 1-0 ta hannun Yakubu Aiyegbeni.

Sai a shekarar 2007 ta ci ta 2-0 ta hannun Stephen Ayodele Makinwa da Ikechukwu Uche da kuma bana da ta samu galaba a kanta da ci 4-2.

Najeriya za ta karbi bakuncin kasar Lesotho a shekarar 2020.