✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan gaba kadan makiya Najeriya za su kunyata – Olumba-Olumba

An bayyana cewa nan ba da dadewa ba duk wadanda suke hana ruwa gudu a kasar nan tare da masu sace dukiyar kasa, asirinsu zai…

An bayyana cewa nan ba da dadewa ba duk wadanda suke hana ruwa gudu a kasar nan tare da masu sace dukiyar kasa, asirinsu zai tonu.

Shugaban wani coci mai suna Olumba Olumba Obu ne ya fadi haka a Kalaba, a sakon da ya aikae wa taron da Majalisar Matasan Afrika da cocinsa suka gudanar.

Olumba ya ce ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu, nan ba da jimawa ba duk wadanda suke wandaka da dukiyar kasar nan, suke sacewa, asirinsu zai tonu.

Shugaban addinin ya ci gaba da cewa “Najeriya kasa ce da Allah Ya azurta da albarkatun kasa da na al’umma, sai dai har yanzu ana fama da matsalar marasa kishi, masu sace dukiyar kasa, lamarin da ya zama abin kaico.”

Ya kara da cewa Najeriya ba abin da take bukata yanzu face wanda zai dora ta a hanyar kwarai, ya dawo da martabarta, ya magance tare da kwato dukiyar kasa da barayin-zaune suka sace. “Kuma duk wadansu masu daukar dawainiyar sace mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa, su ma asirinsu zai tonu,” inji shi.

Ya shawarci matasa su kaurace wa duk wasu ayyuka na ta’addanci kuma kada su biye wa ’yan siyasa da za su yi amfani da su wajen bangar siyasa, a zubar da jini.